Malamin addini ya shiga takarar gwamna a Zamfara ƙarƙashin ADC
Wani fitaccen malamin addini, Sheikh AbdulMutallib Mohammad Gusau, ya shiga takarar gwamnan Jihar Zamfara ƙarƙashin jam’iyyar ADC.
Ya bayyana hakan ne bayan ya yi rajista a Gusau a ranar Litinin.
Malamin ya ce ya shiga siyasa ne!-->!-->!-->!-->!-->…
Ƴan sanda sun kama jami’ansu 6 kan zargin garkuwa da mutane da ƙwatar kuɗaɗe
Rundunar ƴan sandan jihar Edo ta kama wasu mutane tara, ciki har da jami’anta shida, kan zargin garkuwa da mutane da karɓar kuɗi da ƙarfi.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Eno Ikioyedem, ta ce waɗanda ake zargin sun haɗa da jami’ai!-->!-->!-->…
Kotun Tarayya ta ba tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai beli
Ɗan majalisar wakilai, Bello El-Rufai, ya ce wata Babbar Kotun Tarayya a Jihar Kaduna ta ba mahaifinsa, tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, beli.
Bello El-Rufai ya bayyana haka ne bayan zaman kotu da aka hana ƴan jarida shiga.
Ya!-->!-->!-->!-->!-->…
Sojoji sun tabbatar da mutuwar kwamanda da wasu 6 bayan harin Monguno
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani kwamanda da wasu sojoji shida bayan sun daƙile harin ƴan ta’adda a Monguno, Jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar, an ce lamarin ya faru ne a daren 12!-->!-->!-->…
“Ana iya kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin watanni 6” – Ndume
Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce ana iya kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya cikin watanni shida idan gwamnatin tarayya ta nuna cikakken ƙudurin yin hakan.
Ndume ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi a tashar Channels!-->!-->!-->…
El-Rufai Ya Ce Zai Halarci Babban Taron ADC Yayin da Shari’arsa ke Gudana
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa zai halarci babban taron jam’iyyar ADC “a zuciyarsa” yayin da yake fuskantar shari’a.
Ya bayyana hakan ne bayan fitowarsa daga kotun Jihar Kaduna ranar Litinin.
El-Rufai,!-->!-->!-->!-->!-->…
Ƴan Majalisar Tarayya na ADC Sun Buƙaci Tinubu Ya Kori Shugaban INEC
Ƙungiyar ƴan majalisar wakilai na jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya kori tare da gurfanar da shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, bisa zargin nuna son kai kafin zaɓen 2027.
Jagoran ƙungiyar, Afam Ogene ne ya bayyana!-->!-->!-->…
Majalisar Shari’a Ta Musulunci Ta Ƙaryata Labarin Kiran Addu’ar Cire Shugaban INEC
Majalisar ƙoli ta Shari’a a Najeriya (SCSN) ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ta buƙaci Musulmi su yi addu’ar cire shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan.
A wata sanarwa da ta fitar a Kaduna ranar!-->!-->!-->…
Osimhen Zai Ƙarawa Gaban Barcelona Matuƙar Ƙarfi In Ji Yamal
Matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya buƙaci shugabannin kulob ɗin su fifita ɗaukar ɗan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen, kafin kakar wasa mai zuwa.
Rahoton jaridar Fichajes ya bayyana cewa Yamal na kallon Osimhen a!-->!-->!-->…
Bayan Fuskantar Zazzafar Tattaunawa da Al Jazeera, Bwala Ya Ce An Yi Masa Tiyata a Maƙogwaro
Mai ba Shugaban Najeriya shawara kan sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa ya yi tiyatar maƙogwaro kwanaki takwas bayan wata tattaunawa mai zafi da ɗan jarida Mehdi Hasan na Al Jazeera.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar!-->!-->!-->…