The news is by your side.

Mahara a Plateau sun hallaka mutum biyar a wani harin farkon dare da suka kai ranar Lahadi

20

Aƙalla mutum biyar ne suka mutu bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai a daren Lahadi a yankin Fan da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Plateau.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa jaridar BusinessDay cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare yayin da mutanen ke kan hanyarsu ta komawa gida.

Ya ce maharan sun buɗe wuta ba tare da wani gargaɗi ba, lamarin da ya jawo mutuwar mutum huɗu nan take.

A cewarsa, wani mutum guda ya rasu daga baya a asibiti sakamakon raunukan da ya samu.

Sakataren yaɗa labarai na kungiyar Berom Youth Moulders Association, Rwang Tengwong, ya tabbatar da harin a ranar Litinin a Jos.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici tare da kira ga jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen kare rayukan al’umma.

Sai dai kakakin ƴan sandan jihar, Alfred Alabo, bai samu damar tabbatar da harin ba saboda rashin samun shi ta waya.

Harin ya ƙara tayar da hankali a yankin da ke fama da matsalar tsaro a baya-bayan nan.