The news is by your side.

Osimhen Zai Ƙarawa Gaban Barcelona Matuƙar Ƙarfi In Ji Yamal

61

Matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya buƙaci shugabannin kulob ɗin su fifita ɗaukar ɗan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen, kafin kakar wasa mai zuwa.

Rahoton jaridar Fichajes ya bayyana cewa Yamal na kallon Osimhen a matsayin “ɓangaren da babu” a tsarin harin Barcelona.

A cewar rahoton, Yamal ya yi imanin cewa zuwan Osimhen zai ƙara ƙarfin kai hare-hare, tare da buɗe sarari ga ƴan wasan gefe masu fasaha.

Haka kuma yana ganin ɗan wasan zai rage matsin lamba daga tsaron abokan hamayya.

Barcelona na nazarin yiwuwar ɗaukar Osimhen, duk da cewa farashinsa ya haura Yuro miliyan 100, wanda ke zama babban ƙalubale.

Ɗan wasan ya koma Galatasaray a farkon kakar wasa kan kuɗi Yuro miliyan 75, kuma ya ci gaba da jan hankalin manyan ƙungiyoyi a Turai.

Osimhen, wanda aka san shi da ƙarfi da saurin motsi da kuma iya cin ƙwallo, ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ƴan gaba a Turai.

A kakar wasa ta bana, ya zura ƙwallaye 26 a gasa daban-daban, abin da ya ƙara masa daraja a kasuwar saye da sayar da ƴan wasa.

Yamal ya jaddada cewa irin salon wasansa zai kawo sabon salo ga gaban Barcelona, musamman wajen karya bayan manyan kulobs.

Wannan ya ƙara nuna yiwuwar ganin kulob ɗin na ɗaukar matakin gaggawa domin ƙarfafa tawagarsa.