The news is by your side.

Kotun Tarayya ta ba tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai beli

60

Ɗan majalisar wakilai, Bello El-Rufai, ya ce wata Babbar Kotun Tarayya a Jihar Kaduna ta ba mahaifinsa, tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, beli.

Bello El-Rufai ya bayyana haka ne bayan zaman kotu da aka hana ƴan jarida shiga.

Ya ce iyalansu na ƙoƙarin cika sharuɗɗan belin da kotun ta gindaya.

A cewarsa, “muna farin ciki cewa Malam ya samu beli, kuma za mu cika sharuɗɗan domin mun yi imani da bin doka.”

Ƙoƙarin jin ta bakin lauyan wanda ake ƙara, Ubong Akpan (SAN), bai yi nasara ba, domin ya ƙi yin ƙarin bayani.

Sai dai ya ce babban lauyan shari’ar ne zai yi wa manema labarai ƙarin haske nan gaba.

Shi ma wani jigo a jam’iyyar ADC kuma na kusa da El-Rufai, Hayatudeen Lawal Makarfi, ya tabbatar da batun bayar da belin.

Ya ce an gindaya wasu sharuɗɗa, kuma yana sa ran za a cika su cikin ƙanƙanin lokaci.

Tun da farko dai hukumar ICPC ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu kan wasu tuhume-tuhume.

A zaman da ya gabata a kotun jiha a yau, kotun ta ɗage sauraron buƙatar belin zuwa ranar 21 ga Afrilu, 2026.