Ƴan Majalisar Tarayya na ADC Sun Buƙaci Tinubu Ya Kori Shugaban INEC
Ƙungiyar ƴan majalisar wakilai na jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya kori tare da gurfanar da shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, bisa zargin nuna son kai kafin zaɓen 2027.
Jagoran ƙungiyar, Afam Ogene ne ya bayyana matsayar a Abuja bayan wani taro.
Ogene ya ce kalamai da wasu ayyuka da ake dangantawa da shugaban INEC sun jefa shakku kan gaskiyarsa.
Ya ce akwai zargin cewa ya taɓa bayyana goyon baya ga jam’iyyar APC a wani shafin X a baya.
Ko da yake INEC ta musanta mallakar shafin, rahotanni na bincike sun nuna yiwuwar hakan gaskiya ne.
Wannan ya janyo tambayoyi kan gaskiyarsa da riƙon amanarsa a irin wannan muhimmin muƙami na ƙasa.
Haka kuma rikicin shugabanci a jam’iyyar ADC ya ƙara tsananta, musamman bayan INEC ta janye amincewa da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, a matsayin shugaban jam’iyyar.
Ƴan majalisar sun zargi hukumar da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar, wanda ka iya hana ta tsayar da ƴan takara a zaɓen 2027.
Sun kuma yi zargin cewa akwai haɗin baki tsakanin wasu jami’an shari’a da INEC.
Ƙungiyar ta ce za ta miƙa koke ga majalisar shari’a ta ƙasa domin bincikar alƙalai da ake zargi da nuna son kai.
Ta buƙaci ƴan Najeriya su haɗa kai domin kare demokaraɗiyya daga barazana.