The news is by your side.

Malamin addini ya shiga takarar gwamna a Zamfara ƙarƙashin ADC

68

Wani fitaccen malamin addini, Sheikh AbdulMutallib Mohammad Gusau, ya shiga takarar gwamnan Jihar Zamfara ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Ya bayyana hakan ne bayan ya yi rajista a Gusau a ranar Litinin.

Malamin ya ce ya shiga siyasa ne domin ya zama abin koyi ga shugabanni.

Ya ce halin da ƙasar ke ciki ne ya sa ya yanke shawarar shiga harkar siyasa.

A cewarsa, wasu ƴan siyasa ba sa tuna ranar sakamako, wanda ke sa su aikata ba daidai ba.

Ya kuma yi alƙawarin magance matsalar tsaro da talauci idan aka ba shi dama.

Gusau ya soki gwamnatin jihar kan rashin cika alƙawuran da ta yi na inganta tsaro.

Ya ce, “da yardar Allah zan kawo sauyi idan na zama gwamna.”

Malamin ya kuma jaddada cewa zai yi aiki da tsoron Allah a shugabancinsa.

Ya buƙaci magoya bayansa su shiga jam’iyyar ADC domin kawo sauyi a Najeriya.