The news is by your side.

Harin ƴan bindiga ya kashe mutum 11 a Katsina, jami’an tsaro sun fara farautar masu laifin

53

Aƙalla mutum goma sha ɗaya ne suka mutu a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 12 na rana bayan wani harin ramuwar gayya da ƴan bindiga suka kai a ƙauyukan Jeka da Kolo da Kwalgoro a ƙaramar hukumar Kankia ta Jihar Katsina.

Rundunar ƴan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da cewa maharan sun sake haɗuwa ne suka kai farmakin inda suka harbe mutane kafin jami’an tsaro su dawo su fatattake su.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Ali Umar Fage, ya yi Allah-wadai da harin tare da jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a daren Lahadi, ya bayyana harin a matsayin na rashin imani tare da bayar da umarnin a kamo masu laifin.

Sanarwar ta ƙara da cewa an tura ƙarin jami’an tsaro tare da ƙarfafa sintiri da bincike domin kamo waɗanda suka tsere.

Rundunar ta kuma buƙaci al’umma su bayar da sahihan bayanai ta lambobin gaggawa 0815 697 7777 da 0707 272 2539 domin taimakawa jami’an tsaro.

Ƴan sanda sun ce harin ya biyo bayan nasarorin da suka samu a baya, ciki har da hana satar shanu a ranar 29 ga Afrilu 2026 a ƙauyukan Gadar Yan Tulu da Kartaka inda aka ƙwato dabbobi 205.

Haka kuma a ranar 2 ga Mayu 2026, jami’an tsaro sun daƙile wani hari a ƙauyen Matinjin tare da ƙwato babura takwas na ƴan bindigar.

Gwamnatin Jihar Katsina ma ta yi Allah-wadai da harin, inda kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida, Nasir Mu’azu, ya ce an kai harin ne kan fararen hula ba tare da sun aikata wani laifi ba.

A cewar gwamnatin, wani fitaccen shugaban ‘ƴan bindiga mai suna Mohammadu Fulani ne ya jagoranci hare-haren, inda aka riga aka samu bayanan sirri game da shirinsu.

Gwamnatin ta yaba da saurin mayar da martanin jami’an tsaro tare da jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin al’umma da hukumomi wajen kare rayuka.