Bayan Fuskantar Zazzafar Tattaunawa da Al Jazeera, Bwala Ya Ce An Yi Masa Tiyata a Maƙogwaro
Mai ba Shugaban Najeriya shawara kan sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa ya yi tiyatar maƙogwaro kwanaki takwas bayan wata tattaunawa mai zafi da ɗan jarida Mehdi Hasan na Al Jazeera.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar News Central a shirin 60 Minutes with Mr Kay.
Bwala ya ce, “Kwanaki takwas bayan hirar, na yi tiyata a maƙogwaro. Ban san ko ƴan Obidient ne suka jefa min wani abu ba, amma yanzu na dawo lafiya.”
Wannan furuci nasa ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.
Ya soki wasu masu amfani da kafafen sada zumunta da ya kira ‘Obidients’, yana mai cewa suna fifita biyayya ga siyasa sama da muradun ƙasa.
A cewarsa, “Akwai wasu da ba su damu da tsaron ƙasa ba, sai dai burin jaruminsu.”
Dangane da hirar, Bwala ya kare kansa, yana mai cewa salon tambayoyin Mehdi Hasan na adawa ne.
Ya ce, “Ya yi ƙoƙarin jan magana domin ya ɓata sunan gwamnati, amma bai samu nasara ba.”
Ya ƙara da cewa yawancin tambayoyin sun shafi kalaman da ya taɓa yi a baya lokacin yana adawa, wanda ya amince da su amma ya buƙaci a kalli gaba.
“Na ma faɗa masa cewa na taɓa faɗin fiye da haka, amma mu mai da hankali kan manufar hira,” in ji shi.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa hirar ta janyo suka sosai a kafafen sada zumunta, musamman bayan Mehdi ya gabatar da bidiyoyi da ke nuna tsoffin kalaman Bwala. Ƙungiyoyi kamar Amnesty International da Human Rights Watch sun kuma fito a cikin tattaunawar kan matsalolin tsaro, inda aka ce Bwala bai gabatar da hujjoji masu ƙarfi ba.