Browsing Category
Manyan Labarai
Labaran da suka fi muhimmanci a kasa da duniya.
BBC na shirin rage ma’aikata kusan 2,000 saboda matsin tattalin arziƙi
Kafar watsa labarai ta BBC ta sanar da shirin rage ma’aikata tsakanin 1,800 zuwa 2,000, wanda ke kusan kashi ɗaya cikin goma na ma’aikatanta, domin fuskantar matsin tattalin arziƙi mai tsanani da yake ciki.
BBC ta ce tana buƙatar!-->!-->!-->…
Abubuwan da suka faru a shekaru uku na yaƙin basasar Sudan na ci gaba da ta da hankalin duniya
Ranar 15 ga Afrilu ta cika shekaru uku da ɓarkewar yaƙin basasa a Sudan tsakanin rundunar sojin ƙasar da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF).
Rikicin, wanda ya samo asali daga taƙaddama kan iko tsakanin Abdel Fattah al-Burhan da!-->!-->!-->…
Gwamnatin Najeriya ta nace cewa harin sojoji kan fararen hula a Borno na da nufin yaƙi da ta’addanci…
Gwamnatin Najeriya ta bayyana harin jirgin sama da aka kai a yankin Jilli na ƙaramar hukumar Gubio a Jihar Borno a matsayin sahihin aiki na yaƙi da ta’addanci ƙarƙashin Operation HADIN KAI.
A cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labarai,!-->!-->!-->…
Jigawa ta amince da sabbin ayyuka a fannoni daban-daban kan biliyoyin nairori
Majalisar zartarwar Jihar Jigawa ta amince da muhimman tsare-tsare da kuɗaɗe a taronta na ranar 13 ga Afrilu, 2026 ƙarƙashin jagorancin gwamna Umar Namadi.
A cewar sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai, Sagir Musa Ahmed, ya fitar,!-->!-->!-->…
Peter Obi ya ce yana da shirin bunƙasa Arewa fiye da sauran ƴan takarar shugaban ƙasa
Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027 da zai iya ba Arewa abin da yake shirin yi.
Ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi a tashar Arise TV ranar Litinin.
Obi ya ce yankin Arewa na da!-->!-->!-->!-->!-->…
Ƴan sanda sun kama jami’ansu 6 kan zargin garkuwa da mutane da ƙwatar kuɗaɗe
Rundunar ƴan sandan jihar Edo ta kama wasu mutane tara, ciki har da jami’anta shida, kan zargin garkuwa da mutane da karɓar kuɗi da ƙarfi.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Eno Ikioyedem, ta ce waɗanda ake zargin sun haɗa da jami’ai!-->!-->!-->…
Sojoji sun tabbatar da mutuwar kwamanda da wasu 6 bayan harin Monguno
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani kwamanda da wasu sojoji shida bayan sun daƙile harin ƴan ta’adda a Monguno, Jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar, an ce lamarin ya faru ne a daren 12!-->!-->!-->…
Ƴan Majalisar Tarayya na ADC Sun Buƙaci Tinubu Ya Kori Shugaban INEC
Ƙungiyar ƴan majalisar wakilai na jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya kori tare da gurfanar da shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, bisa zargin nuna son kai kafin zaɓen 2027.
Jagoran ƙungiyar, Afam Ogene ne ya bayyana!-->!-->!-->…
Majalisar Shari’a Ta Musulunci Ta Ƙaryata Labarin Kiran Addu’ar Cire Shugaban INEC
Majalisar ƙoli ta Shari’a a Najeriya (SCSN) ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ta buƙaci Musulmi su yi addu’ar cire shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan.
A wata sanarwa da ta fitar a Kaduna ranar!-->!-->!-->…
INEC Ta Ɗage Sabunta Rijistar Masu Kaɗa Ƙuri’a a Najeriya Har Sai Bayan Zaɓen 2027
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta sanar da ɗage aikin sake tantance rajistar masu kaɗa ƙuri’a a faɗin kasar har sai bayan babban zaɓen 2027.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, wadda!-->!-->!-->…