The news is by your side.

Jigawa ta amince da sabbin ayyuka a fannoni daban-daban kan biliyoyin nairori

63

Majalisar zartarwar Jihar Jigawa ta amince da muhimman tsare-tsare da kuɗaɗe a taronta na ranar 13 ga Afrilu, 2026 ƙarƙashin jagorancin gwamna Umar Namadi.

A cewar sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai, Sagir Musa Ahmed, ya fitar, majalisar ta amince da shiga shirin Green Nigeria Challenge domin kare muhalli.

Shirin na nufin yaƙi da kwararowar hamada, ƙara yawan itatuwa da inganta rayayyun halittu tare da ƙarfafa haɗin gwiwar al’umma.

Majalisar ta kuma amince da ƙarin ayyuka a aikin gina cibiyar samar da iskar oxygen ta zamani a Dutse domin inganta harkokin lafiya.

An ware sama da naira biliyan 1.22 domin ƙarin kayayyaki, wanda ya sa jimillar kuɗin aikin ta kai kusan naira biliyan 3.43.

Haka kuma majalisar ta amince da rabon naira miliyan 362.8 ga cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 281 a ƙananan hukumomi 27 domin inganta ayyukansu.

An kuma ware naira miliyan 56.67 domin biyan alawus ga ma’aikatan lafiya na gaba-gaba da suka haɗa da ungozoma da jami’an wayar da kan al’umma.

Bugu da ƙari, an amince da kashe sama da naira miliyan 57.44 domin gudanar da ayyukan wannan shiri a matakin jiha.

A ɓangaren makamashi, majalisar ta amince da sake duba kuɗin aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana a muhimman gine-ginen gwamnati.

An ƙara kuɗin aikin daga naira biliyan 6.08 zuwa naira biliyan 7.46 domin faɗada aikin da ƙara ƙarfin samar da wutar lantarki a jihar.

A cewar gwamnatin, waɗannan matakai za su taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati da rage dogaro da tsofaffin hanyoyin samar da makamashi.