The news is by your side.

INEC Ta Ɗage Sabunta Rijistar Masu Kaɗa Ƙuri’a a Najeriya Har Sai Bayan Zaɓen 2027

81

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta sanar da ɗage aikin sake tantance rajistar masu kaɗa ƙuri’a a faɗin kasar har sai bayan babban zaɓen 2027.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, wadda Kwamishinan Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Haruna, ya sanya wa hannu bayan ganawa da Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi.

A cewar sanarwar, hukumar ta tattauna kan shirin a yayin taron, inda daga bisani ta “yanke shawarar ɗage aikin har sai bayan zaɓen 2027.”

INEC ta jaddada cewa wannan shiri muhimmin ɓangare ne na ƙoƙarinta na tabbatar da ingantacciyar rijistar masu kaɗa ƙuri’a a Najeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa aikin zai taimaka wajen tabbatar da sahihancin bayanan masu kaɗa ƙuri’a, kawar da sunayen da suka fito sama da sau ɗaya da waɗanda ba su cancanta ba, tare da ƙara ƙarfin amincin tsarin zaɓe.

Haka kuma zai bai wa masu kaɗa ƙuri’a damar duba bayanansu da gyara duk wani kuskure.

Tun da farko an tsara gudanar da aikin daga ranar 13 ga Afrilu zuwa 19 ga Mayu 2026 a matakai uku, daga ƙananan hukumomi zuwa rumfunan zaɓe.

Sai dai yanzu an ɗage shi domin bai wa shirye-shiryen zaɓen 2027 cikakken tsari kamar yadda hukumar tai iƙirari.

Hukumar ta sake jaddada ƙudirinta na gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, tana mai cewa za a ci gaba da rajistar masu kaɗa ƙuri’a (CVR) daga Afrilu 2026 zuwa Janairu 2027.

Ta kuma bayyana cewa za a ci gaba da amfani da fasahohin BVAS da tsarin aika sakamakon zabe na zamani.

A ƙarshe, INEC ta sanar da cewa zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya zai gudana ranar 16 ga Janairu 2027, yayin da na gwamnoni da majalisun jihohi zai biyo baya a ranar 6 ga Fabrairu 2027.