The news is by your side.

“Ban gama yanke shawarar barin ADC ba, ina dai tattaunawa da NDC da PRP kan neman mafita,” – Kwankwaso

67

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce bai yanke hukunci kan makomar siyasarsa ba duk da raɗe-raɗin cewa zai fice daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Asabar, Kwankwaso ya ce yana ci gaba da tuntuɓa da jam’iyyu da dama ciki har da National Democratic Congress, NDC, da Peoples Redemption Party, PRP.

Wannan na zuwa ne bayan abokinsa Buba Galadima ya shaida wa manema labarai a ranar 2 ga Mayu, 2026 cewa Kwankwaso da Peter Obi za su fice daga ADC.

Kwankwaso ya ce matsalolin shari’a da ke addabar ADC sun haɗa da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya soke wani taron jam’iyyar.

Ya kuma ambaci buƙatar da Babban Lauyan Tarayya ya gabatar na soke rajistar jam’iyyar a matsayin wata babbar barazana.

Kwankwaso ya ce, ya bar jam’iyyar NNPP ne saboda irin waɗannan matsaloli na shari’a da suka sanya zamansa a cikinta ya zama mai haɗari.

Dangane da batun takarar shugaban ƙasa, ya ce ADC ba ta yanke hukunci kan yankin da za ta ba tikitin takara ba har yanzu.

Ya ƙara da cewa bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba kuma bai goyi bayan wani ɗan takara ba.

Kwankwaso ya ce rashin halartarsa a wasu tarukan jam’iyyar na baya-bayan nan ya faru ne saboda wasu dalilai na ƙashin kai.

Ya ce zai bayyana matsayinsa kan makomar siyasarsa nan gaba kaɗan.