The news is by your side.

Peter Obi ya bayyana dalilan ficewarsa daga ADC, ya zargi tsarin siyasar Najeriya da matsaloli

70

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana dalilan ficewarsa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

A cikin saƙon da ya wallafa bayan halartar ibada a ranar Lahadi, Obi ya ce ya yanke shawarar ficewa ne ba saboda wata matsala da shugabannin jam’iyyar ba.

Ya ce bai samu wata matsala kai tsaye daga shugaban jam’iyyar ADC, Sanata David Mark, ko tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ba.

Sai dai ya zargi tsarin siyasar Najeriya da haddasa rikice-rikice a jam’iyyun siyasa, yana mai cewa irin wannan matsala ce ta tilasta masa barin Labour Party a baya.

A cewarsa, “tsarin da ya kamata ya kare jama’a ne ke haifar da tsoro, rashin tsaro da kuma takura ga masu ƙoƙarin yi wa ƙasa hidima.”

Obi ya ce rikice-rikicen cikin gida da shari’o’i da rashin haɗin kai a ADC sun sa ya ga ya dace ya bar jam’iyyar domin samun zaman lafiya.

Ya kuma bayyana cewa yana fuskantar suka da matsin lamba duk da ƙoƙarinsa na inganta Najeriya.

Obi ya ce ba ya neman muƙamin shugaban ƙasa ko wani matsayi, amma yana son ganin Najeriya ta zama ƙasa mai adalci da walwala.

Ya ƙara da cewa yana da yaƙinin cewa Najeriya na da damar ci gaba idan aka samu shugabanci nagari da gaskiya.