The news is by your side.

JAMB ta ba da haƙuri kan jinkirin fitar sakamakon UTME, ta ce yau Lahadi zai fita

78

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya (JAMB) ta ba da haƙuri kan jinkirin fitar da sakamakon rukunin ɗaliban da suka rubuta jarabawar UTME a ranar Juma’a 17 ga Afrilu, 2026, tana mai tabbatar da cewa za a fitar da su kafin ƙarshen ranar Lahadin nan.

Hukumar ta bayyana a baya cewa, za a saki sakamakon a ranar Asabar, amma jinkirin ya haifar da damuwa ga ɗaliban da ke jiran sakamakonsu.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fabian Benjamin, ya fitar a yau Lahadi, ya ce jinkirin ya faru ne sakamakon rashin kasancewar shugaban hukumar wanda ya je wani muhimmin aiki na hukuma.

Ya ƙara da cewa an shawo kan matsalar, kuma za a fitar da sakamakon kafin dare ya yi.

“Mun yi matuƙar nadamar jinkirin fitar da sakamakon ranar Juma’a 17 ga Afrilu, kuma muna tabbatar da cewa za a fitar da su kafin dare,” in ji Fabian Benjamin a cikin sanarwar.

Hukumar ta kuma nemi afuwar ɗaliban da suka kwana suna jiran sakamakon, tare da gode musu kan haƙurinsu da fahimtar da suka nuna.

Tun da farko, JAMB ta fitar da sakamakon ɗaliban da suka rubuta jarabawar ranar Alhamis 16 ga Afrilu, inda sama da ɗalibai 600,000 suka samu nasu sakamakon.

An buƙaci ɗalibai su duba sakamakonsu ta hanyar tura saƙon “UTMERESULT” zuwa 55019 ko 66019 da lambar wayar da suka yi rijista da ita.

A ranar Asabar, shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce an samu ƙarancin matsaloli yayin gudanar da jarabawar a faɗin Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar duba cibiyoyin jarabawa na CBT a Jami’ar Ibadan da ke Ibadan, Jihar Oyo, inda ya ce daga cibiyoyi kusan 980, kusan 16 ne kawai suka fuskanci matsaloli.

Farfesa Oloyede ya ƙara da cewa sama da dalibai miliyan 1.7 aka yi wa jarabawa cikin kwanaki uku kuma cikin nasara, yana mai yabawa da yadda aka gudanar da aikin.