The news is by your side.

Jam’iyyun adawa sun amince da tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda a zaɓen 2027

58

Wani ɓangare na shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Kabiru Tanimu-Turaki, ya sanar da cewa jam’iyyun adawa sun amince su tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda a zaɓen 2027.

Turaki ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a taron ƙoli na jam’iyyun adawa da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, inda shugabanni daga jam’iyyu daban-daban suka hallara.

Ya ce matakin na da nufin ƙarfafa damar jam’iyyun adawa a zaɓe duk da abin da ya kira ƙoƙarin jam’iyyar APC na tabbatar da Shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takara ɗaya tilo.

A cewarsa, “duk da ƙoƙarin jam’iyya mai mulki na tabbatar da Tinubu a matsayin ɗan takara ɗaya tilo, mu ma za mu tsayar da ƴan takara mu fafata a zaɓen 2027.”

Ya ƙara da cewa, jam’iyyun adawa sun ƙuduri aniyar haɗa kai domin fitar da ɗan takara guda da zai samu goyon bayan dukkan ɓangarori.

Har ila yau, shugabannin sun buƙaci shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya yi murabus bisa zargin nuna ɓangaranci ga APC.

Sun yi gargadin cewa, ci gaba da riƙe muƙamin nasa na iya kawo cikas ga sahihancin zaɓen 2027 da kuma tayar da rikici.

Taron ya kuma mayar da hankali kan haɗin kai da gyaran tsarin zaɓe domin inganta demokaraɗiyya a Najeriya.