The news is by your side.

Matthew Kukah ya ce a daina kiran sa Bahaushe, shi ɗan Najeriya ne daga Zangon Kataf a Jihar Kaduna

42

Bishop na cocin Katolika a Sokoto kuma shugaban jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu University (COOU), Most Rev. Dr. Matthew Hassan Kukah, ya buƙaci ƴan Najeriya su daina kiran sa Bahaushe, yana mai cewa shi cikakken ɗan Najeriya ne daga Jihar Kaduna.

Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin bikin yaye ɗalibai karo na 16 da aka gudanar a ɗakin taro na jami’ar da ke Igbariam, Jihar Anambra.

Kukah ya ce, “ni ɗan asalin Anchuna ne a masarautar Ikulu da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, amma ba Bahaushe ba ne na asali, don haka ya kamata a daina kirana haka.”

Sabon shugaban jami’ar ya kuma yi alkawarin yin aiki tuƙuru domin cika burin jami’ar, yana mai jaddada muhimmancin tarbiyya ga ɗaliban da suka kammala karatu.

Ya yabawa gwamnatin Jihar Anambra kan zuba jari a ɓangaren ilimi, yana mai cewa a ƙididdiga ta nuna jihar na cikin sahun gaba a ilimi a tsakanin jihohin Najeriya 36.

Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, wanda ya naɗa Kukah a matsayin shugaban jami’ar, shi ne ya rantsar da shi a hukumance a wurin bikin.

Soludo ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa ƙwarewa da jagorancin Kukah za su ƙara bunƙasa matsayin jami’ar.

Ya ƙara da cewa bikin ya nuna muhimmancin jami’o’i wajen horas da ƙwararru da kuma gina tarbiyya a cikin al’umma.

A yayin taron, gwamnan ya bai wa ɗalibin da ya fi fice, Somtochukwu Augustus Ume daga sashen tattalin arziƙi, kyautar naira miliyan 4 bayan ya samu darajar 4.85 daga 5.0.

Haka kuma ya sanar da ba wa ɗalibai 37 da suka kammala da digiri ajin farko tallafin karatu domin ci gaba da karatun digiri na gaba a jami’o’in gwamnati.