Iran da Amurka sun samu ci gaba a tattaunawar zaman lafiya amma ‘da sauran tafiya’ in ji Ghalibaf
Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce an samu ci gaba a tattaunawar da ake yi da Amurka, amma har yanzu akwai tazara mai yawa kafin cimma yarjejeniya ta ƙarshe.
Ghalibaf ya bayyana hakan ne a wani jawabi da aka yaɗa a talabijin a daren Asabar, yana mai cewa har yanzu akwai muhimman batutuwa da ba a warware ba.
A ranar Lahadi, shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya ce, shugaban Amurka Donald Trump ba shi da hurumin hana Iran amfani da haƙƙoƙinta na sarrafa makamashin nukiliya.
“Trump yana cewa Iran ba za ta yi amfani da haƙƙoƙinta na nukiliya ba, amma bai bayyana mana laifin da muka aikata ba,” a cewar Pezeshkian kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iranian Student News Agency ya rawaito.
Batun shirin nukiliyar Iran da kuma mashigin ruwa na Hormuz na daga cikin manyan matsalolin da ke hana cimma yarjejjeniya har yanzu.
Rundunar IRGC ta Iran ta sake ƙaƙaba takunkumi a mashigin Hormuz ƙasa da awanni 24 bayan buɗe shi, tana mai danganta hakan da ci gaba da toshe tashoshin jiragen ruwan Iran da Amurka ke yi.
Ghalibaf ya kira wannan mataki na Amurka da “rashin hankali”, yana mai cewa, Iran ba za ta bari wasu su riƙa wucewa ta mashigin ba idan an hana nata jiragen.
Ya kuma yi gargaɗin cewa, dakarun Iran na cikin shiri don fuskantar duk wani sabon yaƙi da Amurka.
A cewar wakilin Al Jazeera Tohid Asadi daga Tehran, Iran na amfani da mashigin Hormuz a matsayin wani muhimmin makami na matsin lamba a tattaunawar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar sake kai hare-hare idan ba a cimma yarjejeniya kafin ranar Laraba ba, lokacin da wa’adin tsagaita wuta zai ƙare.
Sai dai jami’an diflomasiyya na ci gaba da ƙoƙarin shirya zagaye na gaba na tattaunawar bayan wanda aka yi a Islamabad a ranar 12 ga Afrilu bai kai ga cimma matsaya ba.