The news is by your side.

Gwamnatin Najeriya ta amince da ƙarin alawus-alawus da sabbin tsare-tsaren jin daɗin ma’aikata

207

Gwamnatin Najeriya ta sanar da amincewa da ƙarin alawus-alawus na musamman da sauran tsare-tsaren jin daɗin ma’aikata domin ƙara inganta albashin ma’aikatan gwamnati da kuma ƙarfafa ƙwarin gwiwarsu.

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.

Ta ce Majalisar Zartarwa ta Tarayya ce ya amince da gyaran, wanda ya shafi ma’aikata da ke ƙarƙashin tsarin albashi na CONPSS da kuma CONRAISS.

A cewarta, an tsara ƙarin alawus-alawus ɗin ne ta yadda zai shafi dukkan matakan aiki, daga ƙananan ma’aikata zuwa manya.

Ta ƙara da cewa an kuma amince da ƙarin kuɗaɗen alawus irin su na tafiya aiki (DTA), estacode da kuma kuɗin sayen littattafai.

“Ko da kana Abuja kuma ka halarci horo a cikin Abuja, kana da damar karɓar cikakken DTA,” in ji Didi Walson-Jack.

Ta bayyana cewa an sake duba kusan dukkan alawus-alawus da ke cikin dokokin aikin gwamnati.

Bugu da ƙari, gwamnatin ta amince da sabon tsarin kuɗin ritaya wanda zai bai wa ma’aikatan da suka yi ritaya kashi 100 na jimillar albashinsu na shekara a matsayin kyautar barin aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026.

Walson-Jack ta ce matakin zai tabbatar da cewa ma’aikata suna barin aiki cikin mutunci da cikakken tallafin kuɗi.

Haka kuma, gwamnatin ta fara aiwatar da shirin bayar da diyya ga ma’aikata da ke fuskantar haɗurra ko rasuwa a wurin aiki.

Masana sun ce waɗannan sauye-sauye na zuwa ne yayin da ake ƙara kira daga ƙungiyoyin ƙwadago na a inganta jin ɗaɗin ma’aikata saboda tsadar rayuwa.