The news is by your side.

Matasa Sun Mamaye Ofishin INEC a Lagos, Sun Nemi Shugaban Hukumar Ya Sauƙa

53

Matasa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) sun gudanar da zanga-zanga a ofishin Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) da ke Yaba a Jihar Lagos a ranar Litinin.

Masu zanga-zangar sun nemi Shugaban hukumar na ƙasa, Joash Amupitan, ya yi murabus bisa zargin aikata rashin gaskiya.

Sun riƙa ɗaga kwalaye masu rubuce-rubuce irin su “INEC ba ta siyarwa ba ce” da “Amupitan ya riga ya lalace,” a cewar rahotanni daga wurin.

Zanga-zangar ta samu jagorancin mataimakin shugaban matasa na ƙasa, Adeola Olusi, tare da tsauraran matakan tsaro a wurin.

A baya, Balarabe Rufai ya sanar da cewa za a gudanar da zanga-zanga a Lagos da Ogun mai taken “Operation Occupy INEC.”

Ya ce matasa suna neman a girmama bin doka tare da dawo da shugabancin ADC da ke ƙarƙashin Sanata David Mark.

Wannan na zuwa ne bayan INEC ta dakatar da amincewa da wasu ɓangarorin ADC a ranar 1 ga Afrilu bisa hukuncin kotu.

A ranar 8 ga watan watan Afrilun nan kuma, manyan ƴan siyasa irin su Atiku Abubakar da David Mark sun gudanar da makamanciyar zanga-zangar a Abuja.

INEC ta ce tana bin hukuncin kotu ne kan rikicin shugabancin jam’iyyar, wanda har yanzu ke ci gaba da haifar da cece-kuce.