Trump Ya Musanta Zargin Jan Shi Ya Shiga Yaƙin Iran, Ya Kare Kansa Da Cewa Raɗin Kansa ne Ya Kai Shi
Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta cewa Isra’ila ce ta janyo shi cikin rikicin yaƙi da Iran, yayin da ake ci gaba da suka kan matsayinsa a rikicin a ranar Litinin.
Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ya yanke hukunci ne bisa hare-haren ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da kuma ra’ayinsa na hana Iran mallakar makamin nukiliya.
Sai dai babu wata hujja ta bayyane da ke danganta Iran kai tsaye da harin Hamas na 7 ga watan Oktoba, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Haka kuma shugabar leƙen asirin Amurka Tulsi Gabbard ta shaida wa majalisar ƙasa a watan Maris cewa Iran ba ta ƙera makamin nukiliya ba.
Rikicin ya tsananta ne bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya yi sanadin mutuwar jagoran Iran Ali Khamenei da wasu jami’ai.
Iran ta mayar da martani ta hanyar rufe mashigar Hormuz, lamarin da ya janyo tashin farashin mai a duniya.
Rahoton NBC News ya nuna cewa, kusan kashi biyu cikin uku na Amurkawa ba su gamsu da yadda Trump ke tafiyar da yaƙin ba.
Tsohuwar mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta ce ana jan Trump cikin yaƙin ne saboda matsin lamba daga Isra’ila.
Trump ya kuma soki kafafen yaɗa labarai, yana zargin su da yaɗa ƙarya kan yadda ake bayyana rikicin da Iran.