The news is by your side.

Ma’aikatan Jigawa sun koka kan rashin daidaita albashinsu bayan sauya musu wuraren aiki da shekaru

115

Wasu ma’aikatan gwamnati a Jihar Jigawa sun koka kan rashin daidaita albashinsu duk da cewa an sauya musu wuraren aiki zuwa wasu wuraren.

Rahotanni sun nuna cewa an sauya wasu ma’aikatan daga asibitoci zuwa kwalejojin koyar da aikin jinya, yayin da wasu kuma aka sauya su daga ƙananan makarantu zuwa manyan makarantu sakamakon ƙarin ƙwarewar da suka samu.

Sai dai ma’aikatan sun ce duk da ƙarin nauyin aiki da ke kansu, ana ci gaba da biyansu tsohon tsarin albashi na wuraren da suka bari.

A cewar wasu daga cikinsu da suka nemi Hausa Times ta ɓoye sunayensu, wannan yanayi ya jefa su cikin matsin rayuwa mai tsanani.

Sun ce wasu daga cikinsu sun shafe shekaru da dama ba tare da an sauya musu tsarin albashin zuwa wanda ya dace da sabon aikinsu ba.

Rahotanni sun ce sama da ma’aikatan jinya 50 aka tura Kwalejin Koyon Aikin Jinya ta Jihar Jigawa a cibiyoyinta uku da ke Birnin Kudu da Babura da Hadejia domin cike giɓin malamai.

A tsarin aiki na yau da kullum, ana sauya tsarin albashin irin waɗannan ma’aikata daga CONHESS zuwa COMPACASS, amma ma’aikatan sun ce ba a yi musu hakan ba har tsawon sama da shekaru biyar yanzu.

Sun kuma ce duk ƙoƙarin da suka yi na tuntuɓar hukumomi domin a aiwatar da sauyin bai haifar da sakamako ba, face alƙawuran baki da ba a cika ba.

A cewarsu, suna ɗaukar nauyin koyarwa, gudanar da ayyukan kwaleji, da kula da ɗalibai, ciki har da shirye-shiryen tantance makarantu da hukumomi kamar NMCN da NBTE ke yi.

Sai dai sun ce ana ba su amsoshi masu karo da juna daga jami’an gwamnati, ciki har da cewa takardunsu sun ɓace ko ba a saka su cikin kasafin kuɗi ba a duk shekara.

Ma’aikatan sun ce wannan jinkiri ya rage musu ƙwarin gwiwa tare da barazana ga ɗorewar ayyukan ilimi a kwalejojin.

Haka su ma waɗanda aka ɗauke daga makarantun manyan sikandire zuwa kwalejojin ilimi da ke Gumel, Ringim da kuma wasu zuwa kwalejojin fasaha da ƙirƙire da ke Dutse, Hadejia da Kazaure da ma waɗanda aka kai jami’ar jihar da ke Kafin Hausa sun yi makamancin wannan kuka.

Ma’aikatan sun buƙaci gwamnati da ta gaggauta sauya tsarin albashinsu tare da biyan dukkan bashin da suke bi, tare da tabbatar da gaskiya da riƙon amana a aikin gwamnati a jihar.