The news is by your side.

Italiya ta dakatar da yarjejeniyar tsaro da Isra’ila saboda yaƙin da take a Lebanon

26

Firaministar Italiya, Giorgia Meloni, ta sanar da dakatar da sabunta yarjejeniyar tsaro da Isra’ila, wadda ta shafi musayar kayan aikin soja da binciken fasaha.

Meloni ta bayyana hakan ne ranar Talata a wani taro da aka gudanar a Verona, kamar yadda kamfanonin dillancin labarai na ANSA da AGI suka ruwaito.

Ta ce, “dangane da halin da ake ciki a yanzu, gwamnati ta yanke shawarar dakatar da sabunta yarjejeniyar tsaro da Isra’ila kai tsaye.”

An amince da yarjejeniyar ne tun a shekarar 2006, kuma ana sabunta ta kai tsaye duk bayan shekaru biyar.

Yarjejeniyar na kunshe da hadin gwiwa a fannonin masana’antun tsaro, horas da sojoji, bincike da ci gaban fasaha da kuma fasahar sadarwa.

Gwamnatin Meloni, wadda ke da ra’ayin mazan jiya, na daga cikin manyan ƙawancen Isra’ila a Turai, duk da cewa a baya-bayan nan ta fara sukar hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon.

Har zuwa yanzu, babu wani martani kai tsaye daga gwamnatin Isra’ila kan wannan mataki.

Tashin hankalin ya ƙaru ne bayan Italiya ta zargi sojojin Isra’ila da harba bindiga a matsayin gargaɗi ga ayarin dakarunta masu aikin wanzar da zaman lafiya a Lebanon.

Rahotanni sun ce lamarin ya janyo lalacewar wata mota, amma babu wanda ya jikkata.

Italiya ta gayyaci jakadan Isra’ila domin nuna rashin jin daɗinta, yayin da Isra’ila ita ma ta gayyaci jakadan Italiya bayan kalaman ministan harkokin wajen ƙasar, Antonio Tajani.

Tajani ya bayyana hare-haren Isra’ila a Lebanon a matsayin “marasa karɓuwa,” yana mai cewa ya je Beirut domin nuna goyon bayan Italiya ga fararen hula.