Browsing Category
Manyan Labarai
Labaran da suka fi muhimmanci a kasa da duniya.
Harin Ƴan Bindiga a Kebbi: Gidaje Sun Ƙone, Mutane Sun Tsere
Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai farmaki cikin dare a wasu ƙauyuka a Jihar Kebbi, lamarin da ya jawo asarar rayuka da lalata dukiyoyi.
Harin ya faru ne a daren Lahadi a ƙauyukan Gebe, Kawara da Kalkami a ƙaramar hukumar Shanga.!-->!-->!-->…
Sauyin Siyasa a Kebbi: Aminu Bande Ya Fice Daga PDP, Ya Koma ADC
Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kebbi na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC bayan ya fice daga PDP.
An karɓe shi ne a hukumance a sakatariyar jam’iyyar ADC ta jihar a ranar!-->!-->!-->…
Atiku Ya Ɗauki Kamfanin Kyautata Alaƙa na Amurka Aiki Gabanin Zaɓen 2027
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya rattaba hannu kan kwangilar dala miliyan 1.2 da wani kamfanin gyaran alaƙa a Amurka domin ƙarfafa matsayinsa a siyasa, in ji rahoton PREMIUM TIMES.
Takardun da aka shigar a!-->!-->!-->…
Ban Tsorata Ba – Seun Okinbaloye Ya Maida Martani ga Minista Wike
Ɗan jaridar Channels TV, Seun Okinbaloye, ya bayyana cewa bai tsorata ba duk da kalaman barazana da ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi masa.
Ya bayyana hakan ne yayin shirin siyasa na Sunday Politics.
Ya ce, “Ina so in bayyana!-->!-->!-->!-->!-->…
Wani Hari Ya Yi Sanadin Mutane 17 a Benue, Borno Ma Ta Fuskanci Harin Ƴan Ta’adda
Aƙalla mutane 17 ne suka mutu a wani hari da aka kai a yankin Mbalom na ƙaramar hukumar Gwer ta Gabas a Jihar Benue.
Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun shiga yankin suna harbe-harbe tare da ƙona gidaje.
Lamarin ya janyo asarar!-->!-->!-->!-->!-->…
Sojoji Sun Ceto Mutane 31 Cikin Waɗanda Aka Sace Ranar Lahadin Nan a Kaduna
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto mutane 31 da aka sace yayin ibadar Easter a ƙauyen Ariko da ke Kachia a jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne bayan sojoji sun samu kiran gaggawa game da harin.
A wata sanarwa da hedikwatar sojin!-->!-->!-->!-->!-->…
Naira Ta Ƙara Ƙarfi Kaɗan Yayin Da Kasuwar Musayar Kuɗaɗe Ke Nuna Ɗan Sauyi
Rahoton Channels TV ya bayyana cewa Naira ta fara kasuwancin ranar Litinin a kan naira 1,377.80 kan kowacce dala a kasuwar musayar kuɗaɗen waje ta Najeriya (NFEM).
Wannan ya nuna ƴar ƙaramar ƙaruwa idan aka kwatanta da naira 1,380.79 da!-->!-->!-->…
Sanata Nakudu da Manyan Ƴan Siyasa Sun Karɓi Shahadar ADC Bayan Ficewa Daga APC a Jigawa
Tsohon sanatan Jigawa ta Tsakiya, Sabo Muhammad Nakudu, tare da wasu manyan ƴan siyasa sun sauya sheƙa daga APC zuwa jam’iyyar ADC.
Daga cikin waɗanda suka biyo shi akwai Bala Ibrahim Chamo da Zakari Kafin Hausa, da sauran wasu tsoffin!-->!-->!-->…
Kashi 60 Cikin 100 na Yanke Ƙafafu a Najeriya Na da Alaƙa da Ciwon Suga — Masana
Ƙwararrun likitoci sun bayyana cewa kusan kashi 60 cikin 100 na yanke gaɓɓai a Najeriya na da alaƙa da cutar sikari (diabetes), lamarin da ke ƙara jefa al’umma cikin haɗari.
A cewar rahoton Punch, masanan sun ce rashin kula da cutar na!-->!-->!-->…
BUK Ta Sanar da Rasuwar Matar Prof. Attahiru Jega, An Yi Jana’izarta a Abuja
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta sanar da rasuwar Hajiya Hadiza Attahiru Jega, matar tsohon shugaban jami’ar kuma tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega.
A cikin sanarwar da jami’ar ta fitar a shafukanta na sada zumunta a ranar!-->!-->!-->…