The news is by your side.

Yau Kotun Ƙoli Za Ta Yanke Muhimmin Hukunci Kan Rikicin Shugabanci a ADC, PDP, da LP

100

Ana sa ran Kotun Ƙoli ta Najeriya za ta yanke hukunci a yau kan rikicin shugabanci a jam’iyyun adawa na PDP, Labour Party da ADC gabanin zaɓen 2027.

Kotun ta ɗauki matakin sauraron ƙarar ne cikin gaggawa bayan jadawalin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta fitar domin shirye-shiryen zaɓen 2027.

Mahimman batutuwan da ake dubawa sun haɗa da halaccin shugabanci, iko da bin dokokin kundin tsarin jam’iyya.

Wannan rikici na da tasiri kai tsaye kan ikon jam’iyyun wajen shirya taruka, gudanar da zaɓen fidda gwani da kuma gabatar da ƴan takara ga INEC.

INEC ta tsara cewa za a gudanar da zaɓukan fidda gwani daga ranar 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026.

Masu ruwa da tsaki sun nuna damuwar cewa, hukuncin kotun na iya sauya tsarin jam’iyyun ko kuma jefa su cikin ruɗani.

Masana doka sun ce idan hukuncin ya saɓa wa ɓangarorin, za su iya komawa wasu jam’iyyu domin cika sharuɗɗan lokaci.

Lauya Douglas Ogbankwa ya ce dole ne ƴan siyasa su nemi hanyoyin da za su tsira idan shari’ar ba ta tafi yadda suke so ba.

Shi ma Akintayo Balogun ya ce idan hukuncin ya zo bayan wa’adin INEC, zai iya rasa tasiri a aikace.

Masu sharhi sun yi gargaɗin cewa hukunci mara tabbas na iya haifar da rikici da shari’o’i da dama a cikin jam’iyyun.

Rahotanni sun nuna cewa, wasu ɓangarori na duba yiwuwar komawa jam’iyyu kamar PRP ko NDC domin kauce wa matsalolin cikin gida.

Ana kallon wannan hukunci a matsayin muhimmin lokaci da zai iya tantance makomar haɗakar jam’iyyun adawa kafin babban zaɓen 2027.