The news is by your side.

JAMB ta fitar da ƙa’idojin jarabawar UTME ta 2026 tare da gargaɗin ɗalibai

68

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya, JAMB, ta fitar da tsauraran ƙa’idoji ga masu rubuta jarabawar UTME ta 2026 da za a fara daga ranar 16 zuwa 25 ga Afrilu.

Hukumar ta ce dole ne ɗalibai su bi ƙa’idojin domin kauce wa soke sakamakonsu ko ɗaukar matakin shari’a a kansu.

A cewar bayanan da aka wallafa a shafin JAMB, duk wanda ya shiga ɗakin jarrabawa ba tare da takardar rajista ba za a soke sakamakonsa.

Haka kuma, an haramta shiga da wayar hannu, agogo, ko na’urorin lantarki, inda hukuncin ya haɗa da soke sakamako da gurfanarwa a gaban kotu.

Hukumar ta ce yin kwaikwayo ko rubuta wa wani jarrabawa na jawo dakatarwa daga jarabawar ta shekaru biyu da kuma gurfanarwa.

Ta ƙara da cewa, haɗa baki da wasu ko amfani da kayan da ba a amince da su ba zai haifar da soke sakamako da kuma dakatarwa na tsawon shekaru uku.

Sauran laifuffukan sun haɗa da shiga a makare, fita daga ɗakin jarrabawa ba tare da izini ba, da kuma rashin ɗa’a ga malamai masu sa ido.

JAMB ta kuma bayyana jerin kayayyakin da aka haramta, ciki har da littattafai, kyamarori, na’urorin ɗaukar sauti da kayan ado masu amfani da fasahar zamani.

Hukumar ta ce za a yi cikakken binciken tantance ɗalibai ta hanyar fasahar biometric kafin su shiga jarrabawa.

Ta kuma jaddada cewa ana buƙatar ɗalibai su je cibiyoyin jarrabawa da wuri tare da abin da aka amince da shi kawai.

Za a gudanar da jarrabawar a cibiyoyin CBT da aka tantance a faɗin ƙasar, inda zaman farko zai fara da ƙarfe 8:30 na safe kowace rana.