The news is by your side.

PDP ta tabbata ta Wike bayan Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar tsagin Tanimu Turaki

95

Kotun Ƙoli ta Najeriya ta yi watsi da ƙarar daukaka ƙara da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Taminu Turaki ya shigar a ranar Alhamis.

A hukuncin mafi rinjaye da Mai shari’a Stephen Adah ya karanta, kotun ta bayyana cewa taron ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba 2025 ya saɓa da ingantaccen umarnin kotu.

Kotun ta ce wannan umarni ya fito ne daga Kotun Tarayya da Mai shari’a James Omotosho ya yanke, wanda ya haramta gudanar da taron kafin warware wata taƙaddama da ta shafi tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido.

Alƙalan sun soki ɓangaren Turaki kan zuwa wata kotu mai matsayi iri ɗaya domin neman wani umarni maimakon ɗaukaka ƙara, lamarin da suka kira cin zarafin tsarin shari’a.

Kotun ta ƙara da cewa duk mai aikata irin wannan cin zarafi shi ya jawo kansa, tare da jaddada cewa ƙarar ba ta da wani ƙarfi na doka.

Masu ƙarar, ta bakin lauyansu Paul Erokoro (SAN), sun buƙaci kotun ta soke hukuncin Kotun Daukaka Ƙara da ya soke taron, tare da neman a amince da shi.

Sai dai ɓangaren waɗanda ake ƙara, ciki har da Sule Lamido, sun jaddada cewa batun ya shafi rashin bin umarnin kotu ne ba wai harkokin cikin gida na jam’iyya kaɗai ba.

Rahotanni sun nuna cewa Lamido ne ya fara samun umarnin kotu da ya hana PDP gudanar da taron har sai an ba shi damar tsayawa takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar.

Duk da wannan umarni, jam’iyyar ta ci gaba da gudanar da taron, wanda daga bisani kotunan ƙasa da na ɗaukaka ƙara suka ayyana a matsayin ba bisa ƙa’ida ba.

Kotun Ƙolin ta kuma jaddada cewa, jam’iyyun siyasa dole ne su mutunta doka domin su ne hanya zuwa muƙaman gwamnati, inda ta ce duk wanda ya san da umarnin kotu dole ne ya bi shi.

A hukunci marar rinjaye, Mai shari’a Haruna Samani ya ce batun shugabancin jam’iyya al’amari ne na cikin gida, yayin da Mai shari’a Abubakar Umar ya goyi bayan wannan ra’ayi, duk da cewa sun yi Allah-wadai da rashin bin umarnin kotun.