The news is by your side.

Jigawa ta Ƙaddamar da Sabuwar Jami’ar Kimiyyar Lafiya Bayan Sayen Khadija University

103

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jagoranci bikin karɓar Khadija University da ke Majia a ranar Talata tare da mayar da ita Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Jihar Jigawa (Jigawa State University of Medical and Allied Health Sciences, JUMAHS).

An gudanar da bikin ne a Majia da ke Jihar Jigawa, inda mambobin majalisar zartarwa, ƴan majalisar dokoki, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.

Gwamna Umar Namadi ya ce wannan mataki ya zo ne bayan shirin da gwamnati ta fara kimanin shekaru biyu da suka gabata domin inganta ilimi a jihar.

Ya bayyana cewa sayen jami’ar daga hannun ɗan kasuwa mai zaman kansa na da nufin faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimin likitanci ga matasa a Jigawa da ma Najeriya baki ɗaya.

A cewarsa, gwamnati ta fara inganta gine-gine da kuma samar da ƙwararrun shugabanni domin tabbatar da jami’ar ta zama cikin sahun gaba a ƙasar.

Gwamnan ya ƙara da cewa, jami’ar za ta rage yawan ɗaliban da ake turawa ƙasashen waje domin karatun likitanci, inda ya ce sama da ɗalibai 180 na jihar ke karatu a ƙasashen waje a halin yanzu.

Ya kuma yabawa wanda ya kafa jami’ar a farko, Dakta Musa Adamu Majia, bisa gudunmawar da ya bayar wajen samar da cibiyar.

Sabon mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Mahmoud U. Sani, ya bayyana sauyin a matsayin muhimmin mataki na inganta harkar lafiya da ilimi a jihar.

Ya ce jami’ar ita ce ta farko mallakar jiha a Arewacin Najeriya da ta ƙware a fannin kimiyyar lafiya da alaƙa da ita.

Shugaban kwamitin miƙa jami’ar, Dakta Lawan Yunusa Danzomo, ya ce an gudanar da dukkan matakai cikin tsari da gaskiya domin tabbatar da bin doka.

Ya ƙara da cewa kammala karɓar jami’ar na nuna sabon babi na ci gaban cibiyar ilimi a Jihar Jigawa.