The news is by your side.

Akpabio ya yi zargin ana ɗaukar nauyin rashin tsaro a Najeriya ne saboda zaɓen 2027

50

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi zargin cewa wasu na ɗaukar nauyin rashin tsaro a Najeriya saboda ana tunkarar babban zaɓen 2027.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da hedikwatar Hukumar Haraji ta Ƙasa a Abuja.

Akpabio ya ce ƙaruwar hare-haren tsaro na da alaƙa da siyasa, yana mai cewa bayan zaɓe ana iya samun sauƙi cikin gaggawa.

A cewarsa, wasu na amfani da irin waɗannan hare-hare domin karkatar da hankali.

Ya kuma yabawa shugaba Bola Tinubu kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi, yana mai cewa ba zai bari irin waɗannan matsaloli su hana shi mai da hankali kan shugabanci ba.

Akpabio ya ƙara da cewa jam’iyyar APC na da goyon bayan kusan gwamnoni 32 cikin 36 na jihohin ƙasar.

Ya yi watsi da zargin da ƴan adawa ke yi na cewa ana ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya.

A jawabin nasa, ya zargi ƴan adawa da kasa tsara kansu yadda ya kamata domin lashe zabe.

Ya kuma yi tsokaci kan kiraye-kirayen a sauƙe shugaban INEC, Joash Amupitan, yana mai cewa zargin bai da tushe mai ƙarfi.

Akpabio ya ce duk da cewa kowa na da ƴancin goyon bayan ɗan takara, amma ya kamata jami’an gwamnati su yi aiki da muradin ƙasa baki ɗaya.