The news is by your side.

Sojoji Sun Cafke Masu Sanye da Kakin Bogi, Sun Hallaka Ƴan Ta’adda Uku a Filato

138

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation ENDURING PEACE sun cafke wasu mutane biyu da ke sanye da kayan jami’an tsaro na bogi tare da kashe ƴan ta’adda uku a wasu samame da suka kai a Jos ta Arewa da kuma ƙaramar hukumar Wase a Jihar Filato.

A cewar sanarwar da Kyaftin Polycarp Oteh, jami’in yaɗa labarai na rundunar, ya fitar ga manema labarai a ranar Juma’a, an gudanar da aikin ne bayan tura ƙwararrun dakarun yaƙi da ta’addanci domin dawo da zaman lafiya.

A yankin Dutse Uku da ke Jos ta Arewa, dakarun sun kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:45 na dare, inda suka kama waɗanda ake zargin suna sanye da baƙaƙen kayan sojoji tare da hannu a ƙone-ƙone da haddasa rikici.

Mutane biyu da suka samu raunukan harbin bindiga an kai su asibiti kuma suna cikin yanayi mai kyau, yayin da ake tsare da waɗanda aka kama.

Sanarwar ta ce, “wannan nasara na ƙaryata zargin cewa sojoji na da hannu a rikicin, yana nuna cewa masu aikata laifi na fakewa da kayan jami’an tsaro ne domin ɓata sunan rundunar”.

A wani samame na daban a Karem da ke Wase, dakarun sun yi artabu da ƴan ta’adda da ke hawa babura, inda suka fatattake su tare da kashe uku daga cikinsu.

Rundunar ta jaddada ƙudurinta na kawar da duk wata barazana ga zaman lafiya tare da kira ga al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani abin da ba su yarda da shi ba.

Wannan na zuwa ne bayan hare-haren baya-bayan nan da suka yi sanadin mutuwar mutane 28 ciki har da mata da ƙananan yara, wanda ya ƙara dagula al’amuran tsaro a yankin.