Ko albashin miliyan ɗaya ake ba wa ma’aikaci ba zai wadatar ba idan darajar kuɗi ta lalace – Shugaban Ƙwadago
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta ce ko da ma’aikata suna karɓar albashin naira miliyan ɗaya a wata, ba zai wadatar ba idan darajar naira ta ci gaba da faɗuwa, kamar yadda shugaban ƙungiyar Joe Ajaero ya bayyana ranar Talata a Abuja.
Joe Ajaero ya bayyana hakan ne a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), yana mai cewa hauhawar farashi na rage ƙarfin iya yin sayayyar ma’aikata.
Ya ce tsadar rayuwa da ke ƙaruwa na hana ma’aikata iya biyan buƙatunsu na yau da kullum kamar abinci, sufuri da gidaje.
“Ko da ma’aikatan Najeriya suna samun naira miliyan ɗaya, ba zai yi amfani ba idan naira ba ta da daraja,” in ji shi.
Ajaero ya ƙara da cewa abin da ƙungiyar ke buƙata shi ne kuɗin ƙasa mai ƙarfi da zai iya tallafawa ma’aikata har zuwa ƙarshen wata.
Ya kuma jaddada cewa batun sabon mafi ƙarancin albashi dole ne ya bi matakan doka, yana mai cewa ba za a gaggauta shi saboda dalilan siyasa ba.
Ya ce ƙungiyar za ta fara tattaunawa kan sabon albashi ne a lokacin da ya dace kafin ƙarewar wa’adin tsarin albashin da ake kai a yanzu.
Shugaban na NLC ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin rage raɗaɗin hauhawar farashi da tsadar mai da suka ƙara jefa ma’aikata cikin wahala.
Ya kuma buƙaci samar da ingantacciyar manufar makamashi domin kare tattalin arziƙin ƙasar daga tasirin abubuwan da ke faruwa a ƙasashen waje.
Dangane da ranar Ma’aikata mai zuwa, ya ce duk wata zanga-zanga za ta taƙaita ne ga jihohin da ba su aiwatar da mafi ƙarancin albashi ba.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da fafutukar ganin an inganta walwalar ma’aikata tare da tabbatar da daidaiton tattalin arziƙi a Najeriya.