Gwamnatin Najeriya ta nace cewa harin sojoji kan fararen hula a Borno na da nufin yaƙi da ta’addanci ne
Gwamnatin Najeriya ta bayyana harin jirgin sama da aka kai a yankin Jilli na ƙaramar hukumar Gubio a Jihar Borno a matsayin sahihin aiki na yaƙi da ta’addanci ƙarƙashin Operation HADIN KAI.
A cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya fitar, gwamnatin ta ce harin ba na bazata ba ne, domin yankin ya daɗe yana cikin wuraren da aka haramta zirga-zirgar fararen hula saboda haɗarin tsaro.
Rahotanni sun ce harin ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Gwamnatin ta ce an gudanar da aikin ne bayan samun bayanan sirri da sa ido da suka nuna cewa yankin Jilli, wanda ake kira “Kasu Daulaye”, sansanin ƴan ta’adda ne.
Ta ƙara da cewa, an tabbatar da wannan bayanai bayan kama wani yaro mai shekaru 15 da ake zargi da aikin aika saƙonni ga ISWAP a ranar 12 ga Afrilu 2026.
A cewar gwamnati, gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya taɓa bayyana cewa, kasuwannin Jilli da Gazabure an rufe su shekaru biyar da suka gabata saboda matsalar ƴan ta’adda.
Hukumomi sun ce yankin Bindul zuwa Jilli ya kasance hanyar da ƴan ta’adda ke bi, inda aka samu hare-hare da dama a baya-bayan nan.
Bayan makonni na sa ido, rundunar sojin sama tare da haɗin gwiwar sojojin ƙasa sun tabbatar da kasancewar ƴan ta’adda kafin kai harin.
Gwamnatin Najeriyar ta ba da umarnin gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan lamarin domin tabbatar da gaskiya da ɗaukar matakan da suka dace.
Ta kuma ce za a ƙara inganta matakan kare rayukan fararen hula tare da bayar da tallafin jin ƙai ga waɗanda abin ya shafa.
Gwamnatin ta buƙaci jama’a su bi umarnin tsaro tare da kira ga kafafen yaɗa labarai da su riƙa bayar da rahotanni masu inganci kan batutuwan tsaro.