The news is by your side.

Sojoji sun tabbatar da mutuwar kwamanda da wasu 6 bayan harin Monguno

54

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani kwamanda da wasu sojoji shida bayan sun daƙile harin ƴan ta’adda a Monguno, Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar, an ce lamarin ya faru ne a daren 12 ga Afrilu, 2026.

Sanarwar ta ce dakarun Sector 3 sun fuskanci hari a wani wuri da ake kira Charlie 13.

Sojojin sun yi artabu mai tsanani da ƴan ta’addan, lamarin da ya tilasta musu janyewa daga wurin.

Sai dai bayan an shawo kan harin, kwamandan ya rasu ne sakamakon fashewar wani bam da aka binne a ƙasa.

A cewar rundunar, ya gamu da ajali ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gaban dakarunsa domin tantance halin da ake ciki.

Sanarwar ta ce, “ya mutu tare da wasu sojoji shida bayan abin ya lalata motarsa.”

Rundunar ta bayyana jarumtakar kwamandan, tana mai cewa ya nuna shugabanci nagari da sadaukar da kai.

Ta kuma ce mutuwarsu za ta ci gaba da kasancewa a cikin tarihin rundunar da ƙasa baki ɗaya.

Duk da haka, rundunar ta tabbatar da cewa har yanzu sojoji na ci gaba da riƙe wurin da aka kai harin.