The news is by your side.

Iran ta sake rufe mashigin Hormuz yayin da rikicinta da Amurka ke ƙara tsananta

63

Iran ta sanar da sake rufe mashigin ruwa na Hormuz a ranar Asabar, tana mai cewa matakin martani ne ga ci gaba da killace tashoshin ruwanta da Amurka ke yi.

Sojojin Iran sun ce ikon kula da mashigin, wanda ke ɗaukar kusan kashi 20 na man fetur na duniya, ya koma yadda yake a baya, tare da rahotannin cewa jiragen ruwan yaƙi sun harbi wani jirgin kasuwanci da ya yi ƙoƙarin wucewa.

Rufe mashigin ya zo ne sa’o’i bayan an sake buɗe shi, bayan yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki 10 da Amurka ta shiga tsakani tsakanin Isra’ila da Lebanon.

Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta IRGC ta ce killace tashoshin ruwan Iran da Amurka ke yi na nuni da “fashin teku”, tana mai cewa ikon Hormuz yana ƙarƙashin cikakken kulawar sojojin ƙasarta.

Ta ƙara da cewa, “har sai Amurka ta dawo da cikakken ƴancin zirga-zirga ga jiragen Iran, mashigin zai ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin tsauraran matakai.”

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa zuwa ƙarfe 10:30 na safe agogon GMT a ranar Asabar, jiragen mai da gas guda takwas sun wuce, yayin da wasu da dama suka koma baya sakamakon rashin tabbas.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a ranar Juma’a cewa, yarjejeniyar zaman lafiya na kusa da cimmuwa, amma ya yi gargaɗin cewa hare-haren za su ci gaba idan Iran ba ta amince da sharuɗɗa ba.

Trump ya ce, “mai yiyuwa ba zan tsawaita yarjejeniyar ba… za mu iya komawa kai hare-hare,” yayin da yake magana da manema labarai a cikin jirgin Air Force One.

Sai dai Iran ta ce babu wata ranar da aka amince da ita don sabon zagayen tattaunawar zaman lafiyar, tana zargin Amurka da karya alƙawura.

Masana harkokin sufuri na ruwa, ciki har da John-Paul Rodrigue, sun ce rashin tabbas kan halin da ake ciki ya sa jiragen ruwa da dama ke janyewa daga mashigin.

Wani rahoto daga tashar Al Jazeera ya nuna cewa halin rashin tabbas na ci gaba da hana yin hasashen ko za a cimma yarjejeniya cikin sauƙi.