The news is by your side.

Gwamna Umar Namadi ya jaddada goyon bayansa ga kafafen yaɗa labarai a Jigawa

86

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya karɓi tawagogin Fa’ida Radio Malam Madori da Trimming FM Auyo a ranar Juma’a a Fadar Gwamnati da ke Dutse, inda ya jaddada goyon bayan gwamnatinsa ga kafafen yaɗa labarai.

Tawagar Fa’ida Radio ta je ƙarƙashin jagorancin manajan darakta, Bashir F. Danladi, da shugaban Kwamitin Gudanarwa, Alhaji Ali Abdulkadir, yayin da ta Trimming FM ta samu jagorancin manajanta Mustapha Muhammad.

A jawabin sa, Bashir F. Danladi ya yaba wa gwamnan bisa kyakkyawar alaƙa da kafafen yaɗa labarai, yana mai cewa yana daga cikin gwamnoni masu goyon bayan harkokin yaɗaa labarai a Najeriya.

Ya ce tashar Fa’ida Radio, wadda Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya kafa a watan Janairun 2024, na da burin inganta zaman lafiya, wayar da kan jama’a da kuma yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.

Ya ƙara da cewa, tashar na aiki bisa ƙa’idojin National Broadcasting Commission (NBC) tare da neman ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnati domin isar da manufofi da shirye-shirye ga jama’a.

Da yake mayar da martani, Gwamna Umar Namadi ya ce, gwamnatinsa na da alhakin tallafa wa irin waɗannan kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu saboda rawar da suke takawa wajen samar da ayyukan yi da wayar da kan jama’a.

A nasa ɓangaren, Mustapha Muhammad ya bayyana cewa shirye-shiryen Trimming FM sun yi daidai da manufofin gwamnatin jihar, musamman a fannin noma da kiwo.

Ya ce an kafa tashar ne domin ci gaba da manufofin shirin TRIMING na Bankin Duniya da Gwamnatin Tarayya, wanda ke tallafa wa noman rani da inganta ban ruwa.

Ya ƙara da cewa tashar na wayar da kan manoma kan dabarun noma na zamani da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Gwamna Namadi ya bayyana Trimming FM a matsayin muhimmiyar hanya ta isar da saƙonni ga manoma a faɗin Jihar Jigawa.

Ya ce, “Gwamnatin Jigawa za ta yi aiki tare da wannan tashar domin tabbatar da manoma sun samu bayanan da suka dace a kan lokaci.”