The news is by your side.

Likitoci Zasu Fara Yajin Aikin Sai Baba ta Gani a Duk Faɗin Najeriya

65

Kungiyar likitoci masu neman ƙwarewa, NARD, ta sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani na ƙasa baki ɗaya daga tsakar daren ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026.

Wannan mataki ya biyo bayan dakatar da aiwatar da sabon tsarin alawus-alawus da aka amince da shi bayan yajin aikin 2025.

Shugaban ƙungiyar, Dakta Shuaibu Ibrahim, ya bayyana matakin a matsayin abin takaici, yana mai cewa gwamnati ce ta tilasta su ɗaukar wannan mataki.

Ya ce yarjejeniyar ta haɗa da ƙarin alawus na aiki, aikin dare, aiki a ƙauye da sauran haƙƙoƙi.

Ya ƙara da cewa, an shirya fara aiwatar da tsarin tun Janairu amma aka jinkirta zuwa Fabrairu, sannan yanzu gwamnati na shirin dakatar da shi gaba ɗaya.

A cewarsa, wannan mataki na karya yarjejeniya ne da kuma rusa amincewa tsakanin ɓangarorin biyu.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati da ta janye wannan mataki tare da biyan dukkan haƙƙoƙin da ake binta.

Masana sun yi gargaɗin cewa, yajin aikin zai sake jefa ɓangaren kiwon lafiya cikin matsala, musamman a asibitocin gwamnati da ke dogaro da waɗannan likitoci.