Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya, JAMB, ta sanar da cewa za ta fitar da maki na shiga jami’o’i na shekarar karatu ta 2026/2027 a ranar Litinin 11 ga Mayu 2026.
Mai magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ya ce za a yanke hukuncin ne a taron manufofi na shekara-shekara da za a gudanar a Body of Benchers Auditorium da ke Jabi a Abuja.
Benjamin ya ce Ministan Ilimi, Olatunji Alausa, ne zai jagoranci bayyana sabbin manufofin.
Ya bayyana cewa taron yana tattaro shugabannin jami’o’i, kwalejoji da hukumomin kula da ilimi domin yanke shawara kan tsarin ɗaukar ɗalibai.
A cewarsa, za a tattauna maki mafi ƙaranci da za a amince da shi da kuma ƙa’idojin shiga makarantu.
Haka kuma za a samu wakilcin hukumomi kamar NUC, NCCE da NBTE a taron.
Sanarwar ta ƙara da cewa wasu hukumomi kamar NYSC da NELFund za su gabatar da saƙonnin fatan alheri.
Benjamin ya ce za a kuma gabatar da lambar yabo ta NATAP-M karo na shida domin ƙarfafa bin ƙa’idoji.
Ya ƙara da cewa sanarwar maki mafi ƙanƙanta za ta zo da wuri fiye da shekarar 2025 da aka sanar a ranar 8 ga Yuli.