The news is by your side.

Maimakon ‘Sabon Fata,’ gwamnatin Tinubu ta ‘sabunta wahalar ma’aikata’ in ji Atiku a Ranar Ma’aikata

50

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a ranar Alhamis ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jefa ma’aikatan Najeriya cikin sabuwar wahala duk da alƙawarin “sabon fata” da ta yi a shekarar 2023.

A cikin wata sanarwa da ya fitar domin bikin Ranar Ma’aikata ta 2026, Atiku ya ce ranar ɗaya ga watan Mayu rana ce ta girmama gudunmawar ma’aikata, amma a Najeriya an shiga cikin damuwa maimakon farin ciki.

Ya ce, “Ina rubuta wannan saƙo ne cikin baƙin ciki ga ma’aikacin Najeriya wanda aka yi masa alƙawarin sabunta masa fata amma ya samu sabuntawar wahala.”

Atiku Abubakar ya ce matakin cire tallafin man fetur, duk da muhimmancinsa, an aiwatar da shi ba tare da kyakkyawan shiri ba, wanda ya jefa jama’a cikin matsin rayuwa.

Ya ƙara da cewa hauhawar farashin mai ya jawo ƙarin kuɗin sufuri da abinci, lamarin da ya ƙara tsananta rayuwa ga talakawa.

A cewarsa, gwamnati ta gaza samar da kariya ga marasa ƙarfi kafin aiwatar da wannan tsari, wanda ya sa ma’aikata suke fuskantar mafi nauyin wahalar.

Ya kuma soki yadda aka kashe kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin, yana mai cewa an karkatar da su ga ayyukan da ba su da tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a.

Atiku ya zargi gwamnatin da bai wa wani kamfani da ke da alaƙa da shugaban ƙasa aikin titin Lagos zuwa Calabar ba tare da bin ƙa’idojin neman kwangila ba.

Haka kuma ya ce rage darajar naira ya rage ƙarfin iya siyayyar ma’aikata, inda farashin kayayyaki musamman na waje ya yi tashin gwauron zabi.

Ya kuma soki ƙarin haraji da gwamnati ke yi, yana mai cewa hakan yana ƙara jefa ƴan ƙasa cikin wahala maimakon bunƙasa tattalin arziƙi.

Sai dai ya buƙaci ƴan Najeriya su ci gaba da yin fatan alheri, yana mai cewa ƙasar na da damar samun ci gaba idan aka samu shugabanci nagari.