Tsoffin Ƴan Sanda Sun Yi Zanga-Zanga a Abuja Kan Tsarin Fanshonsu, Sun Rufe Kofar Shiga Fadar Shugaban Ƙasa
A ranar Litinin ɗin nan, ƴan sandan da suka yi ritaya tare da iyalansu a ƙarƙashin dandalin Police Retired Officers Forum of Nigeria (PROF) sun gudanar da zanga-zanga a Abuja, babban birnin Najeriya, kan ci gaba da shigar da ƴan sanda cikin tsarin fansho na Contributory Pension Scheme (CPS).
Masu zanga-zangar sun tare wata kofar shiga fadar Shugaban Ƙasa da ke Aso Rock Villa domin nuna rashin amincewarsu da tsarin.
Sun bayyana CPS a matsayin “na rashin gaskiya, kuma ba bisa ƙa’ida ba, mai nuna wulakanci kuma mai cutar da rayuwa,” a cewar shugabansu Raphael Irowainu, tsohon CSP kuma mai kula da ƙungiyar a matakin ƙasa.
Irowainu ya shaida wa manema labarai cewa manufarsu ita ce neman Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokar ficewar ƴan sanda daga tsarin, wacce Majalisar Ƙasa ta amince da ita a ranar 4 ga Disambar 2025 kuma aka tura wa fadar shugaban ƙasa a ranar 16 ga Maris, 2026.
Ya ce wasu hukumomin tsaro kamar sojoji, DSS, Sojojin Sama, Sojojin Ruwa da NIA sun riga sun fita daga tsarin, inda ya ce amma ƴan sanda sun ci gaba da kasancewa a cikinsa cikin wahala.
A cewarsa, “Manufarmu kawai ita ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan wannan doka domin fitar da ƴan sanda daga wannan tsarin da muke kira na zalunci,” in ji Irowainu.
Zanga-zangar ta biyo bayan irin wadda aka yi a shekarar da ta gabata a gaban Majalisar Ƙasa, inda tsofaffin jami’an suka yi kira makamancin haka kan tsarin na CPS.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a wata sanarwa da mai taimaka masa Jackson Udom ya fitar, ya ce tsarin bai da kyau kuma ya jawo wahala ga jami’an tsaro.
Akpabio ya kuma bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa, Shugaba Tinubu zai amince da dokar, yana mai cewa tsarin bai dace da jami’an tsaro da ke sadaukar da rayukansu ba.