The news is by your side.

Peter Obi ya ce yana da shirin bunƙasa Arewa fiye da sauran ƴan takarar shugaban ƙasa

60

Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027 da zai iya ba Arewa abin da yake shirin yi.

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi a tashar Arise TV ranar Litinin.

Obi ya ce yankin Arewa na da babbar dama ta tattalin arziƙi da ba a yi amfani da ita ba.

A cewarsa, noma na iya samar da kuɗaɗe fiye da man fetur idan aka inganta shi.

Ya ce nasarar siyasa a Arewa ba ta dogara ga goyon bayan manyan ƴan siyasa kaɗai ba.

Obi ya jaddada cewa dole ne a magance talauci, rashin tsaro da matsalolin ilimi da lafiya.

Ya ce yana maraba da haɗin gwiwa da ƴan siyasa amma Najeriya ta fi kowa girma.

A cewarsa, matsalar ƙasar ita ce rashin shugabanci nagari da ke haifar da rarrabuwar kai.

Ya kuma jaddada cewa babu wani ci gaba da zai yiwu ba tare da samar da tsaro ba.

Obi ya ce ya koyi darussa daga ƙasashe daban-daban da za a iya amfani da su a Najeriya.

Ya kuma bukaci gwamnati ta ba ƴan adawa damar yin aiki yadda ya kamata domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana.