Yanda Rashin Wutar Lantarki Ya Ci Gaba da Jefa Ƴan Najeriya cikin Duhu Duk da Alƙawurran Gwamnati
Rahoton da jaridar BusinessDay ta wallafa na musamman ya nuna yadda matsalar wutar lantarki a Najeriya ke ci gaba da ta’azzara duk da alƙawurran da gwamnatin tarayya ta ɗauka tun daga shekarar 2023.
Lokacin da Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya hau mulki a watan Agustan 2023, ya yi alƙawarin cewa ƙasar za ta kai megawatt 6,000 kafin ƙarshen shekarar, yana mai cewa “za a samu haske,” sai dai har yanzu al’umma na jiran cikar wannan alƙawari.
A cewar bayanan Hukumar Tsarin Wutar Lantarki ta Ƙasa mai Zaman Kanta, adadin wutar da ake samarwa a halin yanzu bai wuce megawatt 3,331 ba, wanda bai isa ya wadatar da ƙasar da ke da mutane sama da miliyan 200 ba.
Wannan giɓin ya jefa gidaje cikin tsananin zafi tare da jawo asarar kuɗaɗe ga ƴan kasuwa, inda Bankin Duniya ya ƙiyasta cewa, Najeriya na asarar dala biliyan 29 duk shekara sakamakon katsewar wuta.
A lokacin ziyarar kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki ƙarƙashin jagorancin Sanata Eyinnaya Abaribe, ministan ya sake jaddada ƙudirin gwamnati na kai wa megawatt 6,000 kafin ƙarshen 2024, amma hakan bai tabbata ba.
Matsakaicin samar da wuta mafi girma a ranar 28 ga Disamba 2024 ya tsaya a megawatt 5,229, yayin da mafi girma da aka taɓa samu a ƙasar bai wuce 5,801.6 ba.
Mai ba ministan shawara kan sadarwa, Bolaji Tunji, ya amince da gazawar, yana danganta hakan da ɓarna da aka yi wa muhimman kayan aikin samar da lantarki.
Ya ce, “Haƙiƙa an yi alƙawarin megawatt 6,000, amma ayyukan ɓata-gari sun jawo koma baya. Muna ci gaba da ƙoƙari domin inganta wutar lantarki a ƙasa.”
A ranar 2 ga Maris 2025, Najeriya ta kai megawatt 6,003, mafi girma a tarihi, abin da ya janyo farin ciki daga ɓangaren gwamnati.
Sai dai wannan nasara ta ɗan lokaci ce, domin daga baya adadin ya koma ƙasa da megawatt 5,500, yayin da bayanai suka nuna yana zagayen megawatt 5,000 a halin yanzu.
A halin yanzu, kamfanonin samar da wutar lantarki sun ɗora laifi kan ƙarancin iskar gas, inda samar da wutar ke sauƙa zuwa tsakanin megawatt 2,000 da 3,900.
Ministan ya kuma nemi afuwar ƴan Najeriya, yana mai cewa, “Ina ba da haƙuri ga ƴan Najeriya kan wannan matsala ta wucin gadi da ke jawo wahala, musamman a wannan lokaci na zafi.”
Duk da alƙawarin inganta wutar cikin makonni biyu, rahotanni sun nuna cewa ƴan kasuwa da masana’antu na ci gaba da fuskantar tsadar samar da wutar da kansu.
Matsalolin ƙarancin gas, raunin layukan ɗaukar wuta, da kuma matsalolin kuɗi na kamfanonin rarrabawa na ci gaba da janyo tsaiko a ɓangaren lantarkin Najeriya.