RAHOTO: An Samu Hare-Haren Bam Kusan 2000 a Arewa Maso Gabashin Najeriya Tsakanin 2017 da 2024
Wani sabon rahoto na nazarin ayyukan kawar da nakiyoyi a Najeriya na shekarar 2025 ya nuna cewa an samu jimillar hare-haren ababen fashewa na IED guda 1,934 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya tsakanin 2017 zuwa 2024.
Rahoton, wanda jaridar PUNCH ta samo, ya nuna cewa abubuwan da ake dasawa a kan hanyoyi su ne suka fi yawa a hare-haren a duk tsawon lokacin.
Binciken ya nuna cewa hare-haren da aka fi samu sun haɗa da waɗanda ake dasawa a kan tituna, inda suke zarce waɗanda ake ɗaura wa a jiki ko kuma motoci masu ɗauke da bam.
Wannan ya sanya sun zama barazana mafi tsanani ga tsaro a yankin.
A shekarar 2017 kaɗai, an samu hare-hare 381, wanda shi ne mafi girma, ciki har da guda 165 na kan titi da 211 na masu kai harin ƙunar baƙin wake.
A 2018, adadin ya ragu zuwa 267, yayin da 2019 ya ƙara sauka zuwa 189.
Sai dai a 2020, an sake samun ƙaruwar hare-haren zuwa 249, sannan a 2021 ya kai 281.
Duk da raguwar da aka samu a 2022 zuwa 185, alƙaluman sun sake tashi zuwa 191 a 2023 da kuma adadi iri ɗaya a 2024.
Rahoton ya jaddada cewa ƙungiyoyin ta’addanci sun ci gaba da inganta dabarunsu, inda suke ƙirƙirar hanyoyin tayar da bam masu sarƙaƙiya da haɗari, lamarin da ke barazana ga jami’an tsaro, fararen hula da kuma muhimman kayayyakin more rayuwa.
HAUSA TIMES ta rawaito daga PUNCH cewa, da yake jawabi a wani taron horaswa kan yaƙi da abubuwan IED a Abuja ranar 11 ga Maris, 2026, Mai kula da Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa, Manjo Janar Adamu Laka, ya ce waɗannan na’urori na daga cikin manyan barazanar da sojoji ke fuskanta a Najeriya.
Ya ce, “Daga 2011 zuwa 2017, na ga yadda amfani da IED ya sauya daga sarrafawa ta waya zuwa amfani da wasu abubuwa masu hatsari. Duk lokacin da aka gano hanya, ƴan ta’adda kan ƙirƙiri wata sabuwa.”
Ya ƙara da cewa, “A wani lokaci, muna iya cire bam daga ƙasa, amma daga baya sai su ɗora wani a sama wanda zai fashe da zarar an taɓa na farko. Illarsa tana da muni matuƙa.”