The news is by your side.

Sojoji Sun Ceto Mutane 31 Cikin Waɗanda Aka Sace Ranar Lahadin Nan a Kaduna

63

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto mutane 31 da aka sace yayin ibadar Easter a ƙauyen Ariko da ke Kachia a jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne bayan sojoji sun samu kiran gaggawa game da harin.

A wata sanarwa da hedikwatar sojin ta fitar, an ce sojojin sun yi gaggawar isa wurin tare da taimakon mazauna yankin.

Sun fafata da ƴan ta’addar da suka tsere, inda suka tilasta musu sakin mutanen da suka sace.

Sanarwar ta ce, “Matsin lamba daga sojoji ya sa ƴan ta’addan suka bar mutane 31, ciki har da wani da ya jikkata.”

Sai dai an gano gawar mutane biyar da aka kashe kafin sojojin su isa wajen.

An kuma bayyana cewa wasu daga cikin ƴan ta’addar sun samu raunuka, kamar yadda aka gani daga jinin da suka bari yayin tserewa.

Sojojin sun ce sun ƙara ƙaimi wajen bin su domin kamo sauran.

Babban jami’in rundunar, Manjo Janar Abubakar Wase, na kan gaba wajen sa ido kan ayyukan.

Rundunar ta buƙaci jama’a su ci gaba da bayar da bayanai domin tabbatar da ingancin tsaro.