Rahoton Channels TV ya bayyana cewa Naira ta fara kasuwancin ranar Litinin a kan naira 1,377.80 kan kowacce dala a kasuwar musayar kuɗaɗen waje ta Najeriya (NFEM).
Wannan ya nuna ƴar ƙaramar ƙaruwa idan aka kwatanta da naira 1,380.79 da aka rufe kasuwar da ita a makon da ya gabata.
An ce tsarin Electronic Foreign Exchange Matching System (EFEMS) na taimakawa wajen tabbatar da gaskiya da daidaito a kasuwar.
Wannan ya taimaka wajen daidaita darajar Naira duk da ƙarfin dala a kasuwannin duniya.
Masana sun danganta yanayin kasuwar da abubuwa kamar ajiyar kuɗaɗen waje na Najeriya, wanda ya kai dala biliyan 49.29, tare da hasashen zai kai dala biliyan 51.04 nan gaba kaɗan.
Haka kuma, babban bankin Najeriya ya ci gaba da riƙe ƙimar kuɗin ruwa a kashi 26.5 domin rage hauhawar farashi a ƙasar.
A kasuwannin duniya, yen na Japan ya kusa kai matakin 160 kan dala ɗaya, yayin da rikicin Iran ke ƙara tasiri a kan tattalin arziƙi.
Hakan ya sa masu zuba jari suka fi karkata ga dala a matsayin mafaka a ƙasar.
Ministar kuɗi ta Japan, Satsuki Katayama, ta yi gargaɗin cewa, gwamnati na shirin ɗaukar mataki idan kasuwar ta ci gaba da rikicewa.
Duk da haka, ana ganin ƙarfin dala na iya ci gaba saboda tasirin rikice-rikicen siyasa a Gabas ta Tsakiya.