Browsing Category
Manyan Labarai
Labaran da suka fi muhimmanci a kasa da duniya.
Gwamna Abba Kabir Ya Sha Alwashi Kan Ƙarfin APC, Ya Ce Babu Jam’iyyar da Za Ta Iya Ƙwace Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa babu wata jam’iyya da za ta iya karɓe iko a Kano ko Najeriya face jam’iyyar APC mai mulki, yayin da ake shirin zaɓukan 2027.
Ya yi wannan furuci ne yayin da dubban magoya bayansa!-->!-->!-->…
Atiku Da ADC Sun Yi Allawadai Da Barazanar Da Wike Ya Yi Wa Ɗan Jarida, Sun Nemi Ya Gaggauta Neman…
Jam’iyyar ADC da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun yi kakkausar suka ga kalaman Ministan Abuja, Nyesom Wike, inda ya yi barazanar harbe ɗan jarida Seun Okinbaloye.
Wannan ya biyo bayan wata muhawara a shirin Politics!-->!-->!-->…
Harin Jirage Marasa Matuƙi na Iran Ya Lalata Muhimman Wuraren Kadarorin Amurka a Kuwait
Kadarorin Amurka da ke Kuwait sun shiga cikin sahun wuraren da hare-haren Iran suka shafa a ƴan kwanakin nan, inda aka kai manyan hare-hare ta sama da jiragen marasa matuƙi (drones).
A cewar Al Jazeera, hukumomin ƙasar sun ce, an kai!-->!-->!-->…
Likitoci Zasu Fara Yajin Aikin Sai Baba ta Gani a Duk Faɗin Najeriya
Kungiyar likitoci masu neman ƙwarewa, NARD, ta sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani na ƙasa baki ɗaya daga tsakar daren ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026.
Wannan mataki ya biyo bayan dakatar da aiwatar da sabon tsarin alawus-alawus!-->!-->!-->…
Iran Ta Sassauta Takunkumi a Mashigin Hormuz, Ta Bai wa Jiragen Iraƙi Ƴancin Wucewa
Iran ta sanar da cewa jiragen ruwan Iraƙi za su ci gaba da wucewa cikin ƴanci a mashigin Hormuz, wata muhimmiyar hanya ta safarar makamashi a duniya, a wani sabon mataki na sassauta tsauraran matakan da ta ɗauka.
A cewar rahoton Al!-->!-->!-->…
Peter Obi Ya Yi Gargaɗi Kan Sake Zaɓen Tinubu a 2027 Saboda Gazawa a Wutar Lantarki
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a 2023, Peter Obi, ya buƙaci ƴan Najeriya da kada su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027, yana mai zargin gazawarsa wajen cika alƙawarin samar da isasshiyar wutar lantarki.
Obi!-->!-->!-->…
Sojoji Sun Cafke Masu Sanye da Kakin Bogi, Sun Hallaka Ƴan Ta’adda Uku a Filato
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation ENDURING PEACE sun cafke wasu mutane biyu da ke sanye da kayan jami’an tsaro na bogi tare da kashe ƴan ta’adda uku a wasu samame da suka kai a Jos ta Arewa da kuma ƙaramar hukumar Wase a Jihar!-->…
Jigawa Golden Stars Ta Ɗare Teburin NNL Bayan Hukuncin Ladabtarwa
Gasar neman hawa mataki a rukuni na D na Nigeria National League ta ɗauki sabon salo bayan Jigawa Golden Stars sun hau kan teburi sakamakon hukuncin ladabtarwa.
Hukumar ta bai wa Jigawa maki uku da ƙwallaye uku bayan kama Yobe Desert!-->!-->!-->…
JAMB Ta Ƙaryata Jita-Jitar Ɗage Jarabawa, Ta Kira Sanarwar Da ‘Mugun Nufi’
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya, JAMB, ta ƙaryata wata sanarwa da ke yawo cewa an ɗage jarabawar UTME ta 2026, tana mai bayyana ta a matsayin ƙarya da mugun nufi.
A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Asabar,!-->!-->!-->…