The news is by your side.

Gwamna Abba Kabir Ya Sha Alwashi Kan Ƙarfin APC, Ya Ce Babu Jam’iyyar da Za Ta Iya Ƙwace Kano

45

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa babu wata jam’iyya da za ta iya karɓe iko a Kano ko Najeriya face jam’iyyar APC mai mulki, yayin da ake shirin zaɓukan 2027.

Ya yi wannan furuci ne yayin da dubban magoya bayansa suka taru domin tarbarsa bayan dawowarsa daga Abuja, inda ya halarci wasu muhimman ayyukan jam’iyyar.

Yusuf ya yi watsi da ƙarfin jam’iyyun adawa ciki har da ADC, yana mai cewa APC ce kaɗai jam’iyyar da ke da ƙarfin lashe zaɓe a kowane mataki.

Ya ce, “APC a Kano ita ce jam’iyya mai nasara. Babu wata jam’iyya da za ta iya karɓe Kano da Najeriya, da yardar Allah”.

Gwamnan ya kuma mayar da martani ga masu cewa zai yi falle ɗaya kacal, yana mai jaddada cewa zai sake tsayawa takara a APC.

“Mun yi wa’adi ɗaya a NNPP muka fita. Za mu yi na biyu a APC,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cikakken goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa Kano za ta mara masa baya a 2027.

Shugaban APC na jihar, Umar Doguwa, ya ce taron jama’a da aka gani alama ce ta goyon bayan jama’a ga gwamnan.

Rahotanni sun nuna cewa ayarin gwamnan ya ɗauki sa’o’i kafin isa gidan gwamnati daga filin jirgi sakamakon cunkoson magoya baya.