The news is by your side.

ADC Na Shirin Naɗa Wakilai a Manyan Biranen Duniya Don Bayyana Halin Da Demokaraɗiyyar Najeriya Ke Ciki

64

Jam’iyyar ADC ta bayyana shirin naɗa wakilai a manyan biranen duniya guda 12 domin jawo hankalin duniya kan abin da ta kira tauye demokaraɗiyya a Najeriya.

Wannan mataki na zuwa ne bayan hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, ta dena amincewa da ɓangarorin jam’iyyar biyu ƙarƙashin David Mark da Nafiu Bala.

A cikin sanarwar da kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce za su kafa wata hanyar sadarwa ta musamman mai suna Special Representatives Network domin hulɗa da ƙasashen waje.

Ya zargi cewa, tun daga watan Yulin 2025 ana ƙoƙarin “raunana jam’iyyun adawa da taƙaita harkokin siyasa” a ƙasar.

Bolaji ya ce, wakilan za su yi hulɗa da gwamnatoci, majalisu, kafofin yaɗa labarai da ƴan kasashen waje domin bayyana halin da siyasar Najeriya ke ciki.

Haka kuma za su riƙa bayani kan batutuwan tauye haƙƙin ɗan Adam, sahihancin zaɓe da manufofin jam’iyyar.

Birane kamar Washington DC, London, Berlin, Paris da New York na cikin wuraren da za a naɗa wakilan.

Jam’iyyar ta ce wannan shiri zai taimaka wajen ƙara ƙarfafa martabarta a matsayin wata mafita mai inganci.

Har ila yau, za ta fara tattara bayanai kan hare-hare da cin zarafin ƴan siyasa a faɗin ƙasar domin yin amfani da su.