The news is by your side.

Jigawa Golden Stars Ta Ɗare Teburin NNL Bayan Hukuncin Ladabtarwa

136

Gasar neman hawa mataki a rukuni na D na Nigeria National League ta ɗauki sabon salo bayan Jigawa Golden Stars sun hau kan teburi sakamakon hukuncin ladabtarwa.

Hukumar ta bai wa Jigawa maki uku da ƙwallaye uku bayan kama Yobe Desert Stars da laifin saka ɗan wasan da bai cancanta ba, Shedrack John.

Wannan hukunci ya sauya jadawalin gasar tare da ƙara zafi a wasan ƙarshe na kakar.

Tsoffin jagorori Ranchers Bees yanzu suna fuskantar wasa mai matuƙar muhimmanci a waje da Gombe United, inda dole su yi nasara domin ci gaba da fatan hawa matakin.

A gefe guda, Gombe United na ƙoƙarin kaucewa faɗuwa, wanda ke nufin dukkan ɓangarorin na da buƙatar nasara.

Jigawa Golden Stars kuma za su kara da Kebbi United, inda nasara za ta tabbatar musu da hawa zuwa NPFL, yayin da Kebbi ke neman tsira daga faɗuwa.

Masana sun ce wasan ƙarshe zai kasance mai cike da armashi, domin nasara ba kawai za ta kai ga hawa mataki ba ne, har ma da shiga gasar Super 4 a Ikenne domin tantance zakaran NNL na kakar 2025/2026.