Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta sabunta bayananta inda ta dawo da Sanata David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Binciken da aka yi a shafin yanar gizon hukumar ya nuna cewa an kuma dawo da Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa.
Haka kuma an dawo da Mani Ahmad a matsayin ma’aji, da Akibu Dalhatu a matsayin sakataren kuɗi, da kuma Oserheimen Osunbor a matsayin mai ba jam’iyya shawara kan shari’a.
Tun da farko dai, a watan Afrilu, INEC ta cire sunayen waɗannan shugabanni ne bisa umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara, lamarin da ya haifar da cece-kuce a cikin jam’iyyar.
Sai dai Kotun Ƙoli a ranar Alhamis ta soke wannan hukunci tare da cewa umarnin da aka bayar na wucin gadi ba shi da amfani bayan kammala shari’a.
Kotun ta kuma amince da ɗaukaka ƙarar ɓangaren David Mark, tare da umartar a ci gaba da sauraron ƙarar a Babbar Kotun Tarayya.
Ɓangaren da ke goyon bayan Mark ya bayyana matakin a matsayin nasara ga bin doka da kuma zaman lafiya a cikin jam’iyyar.
Sai dai duk da wannan ci gaba, ƙarar da ke ƙalubalantar shugabancin jam’iyyar na ci gaba da zama a gaban kotu.