The news is by your side.

Jakadun Amurka za su je Pakistan yayin da Abbas Araghchi ya isa Islamabad kan rikicin Iran da Amurka

50

Jakadun Amurka Steve Witkoff da Jared Kushner za su isa Islamabad, Pakistan a ranar Asabar domin tattaunawa da Iran, yayin da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya riga ya isa birnin, a cewar Fadar White House.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da tattaunawar Amurka da Iran ta tsaya cik, inda har yanzu babu tabbacin ko Tehran za ta dawo teburin sulhu.

Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce Iran na da “damar cimma yarjejeniya” idan ta dakatar da shirinta na makamin nukiliya ta hanyoyin da za a iya tabbatarwa.

A wani mataki na matsin lamba, Sakataren baitul malin Amurka Scott Bessent ya sanar da daskarar da kadarorin kuɗaɗen zamani na dala miliyan 344 da ake dangantawa da Iran.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Antonio Costa ya buƙaci a buɗe mashigin ruwa na Hormuz ba tare da wata takura ko haraji ba, bayan tattaunawa da shugabannin Lebanon da Syria.

Ɗan jaridar Al Jazeera Almigdad Alruhaid ya rawaito daga Tehran cewa har yanzu babu shirin tattaunawa kai tsaye a Islamabad, duk da cewa ƙoƙarin samun diflomasiyya na ci gaba.

Haka kuma Osama Bin Javaid daga Islamabad ya ce masu shiga tsakani na Pakistan na nuna fatan samun ci gaba, amma babu cikakken bayani kan tattaunawa kai tsaye.

A yankin Gulf, hukumomin Kuwait sun ce jirage marasa matuƙa guda biyu daga Iraqi sun kai hari a arewacin ƙasar ba tare da jikkata kowa ba, yayin da ministan harkokin cikin gida Abdul Amir al-Shammari ya ce an fara bincike.

A Amurka kuwa, Scott Bessent ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa ba za a tsawaita sassaucin da aka bai wa man Rasha ko Iran ba, tare da ƙaƙaba takunkumi kan kamfanonin jigilar mai kusan 40 da wata matatar mai a China.

Sojojin Amurka sun kuma bayyana cewa, yanzu suna da jiragen yaƙi masu sauƙar ungulu guda uku a Gabas ta Tsakiya, mafi yawa tun bayan mamayar Iraqi a 2003.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya zargi ƙungiyar Hezbollah da ƙoƙarin kawo cikas ga yarjejeniyar zaman lafiya da Lebanon, yayin da rahotanni daga Gaza suka ce hare-haren Isra’ila sun kashe aƙalla Falasɗinawa 12.

Hukumar International Energy Agency ta ce kasuwar iskar gas mai ruwa za ta ci gaba da kasancewa cikin tsanani cikin shekarun 2026 da 2027, yayin da farashin ɗanyen mai ya wuce dala 105 kan kowace ganga a duniya.