The news is by your side.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ƙalubalanci dalilin ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai a Najeriya

33

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa kan yadda Najeriya ke ci gaba da karɓar bashi duk da cire tallafin man fetur.

Sanusi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a taron shekara-shekara na TheNiche 2026 da aka gudanar a birnin Lagos mai taken “Governing the Economy: Choices, Trade-offs, and National Priorities.”

Jawabinsa ya biyo bayan buƙatar Shugaba Bola Tinubu ga majalisar tarayya na neman amincewa da sabon bashin dala miliyan 516 domin aikin hanyar Sokoto zuwa Badagry.

A watan Maris, majalisar dokoki ta amince da buƙatar karɓar bashin waje na dala biliyan 6 domin biyan basussuka da wasu ayyuka.

Sanusi ya ce cire tallafin mai ya zama dole, yana mai cewa ba zai yiwu Najeriya ta ci gaba da tallafa wa matatun mai na ƙasashen waje ba tare da bunƙasa nata ba.

Ya ƙara da cewa yanzu ƙasar ta fara tace manta a cikin gida tare da fitar da kayayyakin mai zuwa Turai, abin da ya bayyana a matsayin alheri ga tattalin arziƙi.

Sai dai ya jaddada cewa ya kamata a fara ganin sauƙin tattalin arziƙi bayan cire tallafin, yana mai cewa “ba za a daina almubazzaranci ba sannan a ci gaba da karɓar bashi.”

A cewarsa, “idan ba a biyan tallafin kuma kuɗin na nan, me yasa ake ci gaba da karɓar bashi, kuma don me ake karɓar bashin?”

Sanusi ya kuma kare wasu manufofi irin su cire tallafi da sassauta tsarin canjin kuɗi, amma ya nuna damuwa kan lokacin aiwatar da su.

Ya ce aiwatar da waɗannan manufofi ba tare da taƙaita yawan kuɗin da ke yawo a tattalin arziƙi ba ya ƙara jefa darajar naira cikin matsin lamba.